Hukumar hana safarar mutane a Najeriya NAPTIP a Birnin Kebbi ta ce ta ceto yara 19 da aka yi safararsu daga yankin Zuru da ke Jihar Kebbi zuwa Calabar a Jihar Kuros Riba.
Yayin da yake gabatar da yara 9 cikin 19 da aka tantance tare da haɗa su iyayensu ga Gwamnan Kebbi, Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
- Za a hukunta iyayen da suka hana yara samun ilimi a Adamawa
- Haɗarin mota ya laƙume rayukan fasinjoji 15 a Kwara
Kwamandan Hukumar NAPTIP na Jihar, Musbau Iya Kaura, ya ce hukumar ce ta ceto yaran daga wasu da suka ƙware wajen fataucin yara a Calabar.
Ya ce, an kama mutane shida da suka haɗa da wata Malamar jami’a a Calabar da laifin aikata safarar tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya.
Ya ƙara da cewa wasu rukunin masu aikata safarar a Calabar akan biya su tsakanin N280,000 zuwa N450,000 ga kowane yaro ga abokan harkar ta su a Kebbi.
“Sun yi wa iyayen yaran ƙarya cewa, an kai su garin Gusau da ke Jihar Zamfara domin neman ilimi, sai dai kuma aka kai yaran Calabar a Jihar Kuros Riba. Sun canza sunayensu sun sayar da su ga wasu mutanen da suke amfani da su don dalilai daban-daban,” in ji shi.
Kwamandan NAPTIP ya ƙara da cewa, a cikin yara 19 da hukumar ta NAPTIP ta ceto, tara ne kaɗai aka tantance kuma sun ba da shaida a gaban kotu a kan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya ce sauran 10 din har yanzu ba su bayar da shaida a gaban kotu ba kuma hukumar ba ta tantance su ba.
“Lokacin da aka kama masu safarar, yayin bincike, sun yi iƙirarin cewa cocin nasu ya ba su izinin kai yaran zuwa reshensu a Calabar, amma shugabannin cocin sun musanta iƙirarin nasu cewa ba su da masaniya game da wannan yarjejeniya,” in ji shi.
Gwamna Idris ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da fataucin yara ba, ya kuma yi gargaɗin cewa za a gurfanar da iyayen da suka yi watsi da ‘ya’yansu tare da masu fataucin.