Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) ta bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin tarayya da kuma Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) su warware rashin jituwar da ke tsakaninsu ko kuma a fuskanci daukar matakin gaggawa daga mambobinta a fadin kasar nan.
Shugaban NANS, Sunday Adedayo, ya ba da wa’adin a Sakkwato jim kadan bayan sanya hannu kan bitar kundin tsarin mulkin kungiyar na shekaru 40 da aka yi nazari a kai a gidan gwamnatin, a gaban Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
- Rikicin Ukraine: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya
- Kotu ta daure miji saboda kara aure ba tare da izinin matarsa ba
Adedayo ya ce, “Kungiyar daliban ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu ta gana da ASUU ta warware matsalar ko kuma ta dauki mataki a kasa baki daya wanda ba a taba ganin irinsa ba daga daliban Nijeriya.
“Halayyar gwamnatin tarayya abin takaici ne kuma abin Allah wadai ne saboda rashin cika alkawarin yarjejeniya tun 1999, lokacin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar da kungiyar malaman.
Kazalika, Mataimakin Shugaban NANS Yazeed Tanko Muhammad ya fada wa BBC Hausa cewa za su rufe dukkan titunan da ke shiga birnin Abuja daga ranar Litinin mai zuwa idan ba a janye yajin aikin ba.
“Zanga-zanga ce da idan muka fara ta ba za mu daina ba har sai malamai sun dawo bakin aiki, har sai mun samu mafita,” in ji shi.
“Muna kira ga shugaban kasa da shi ma ya nuna mana goyon baya ya zauna a gida, kar ya je aiki ranar Litinin din”
A farkon makon da ya gabata ne Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na wata daya bayan ta zargi gwamnatin tarayya da rashin mutunta yarjejeniyar da suka kulla tun a 2009 da kuma sabuwa a 2020.