Tabbas taimakon mace ya fi taimakon namiji muhimmanci, musamman idan muka dubi yadda mata da dama a birane da kauyuka ke fama da tsananin talaucin! Abin ya kai ga wasu ba sa samun abinci yadda ya kamata, musamman a Arewacin Najeriya.
Sau da yawa idan magidanta sun sami kudi su kan je tugufa a sayi tsire, balango, indomi, kosai, ko ma a kashe kwai, a sha shayi! Yayin da uwar gida da ‘ya’yanta na gida wani ma daga layya sai layya suke dandana nama! Ba a damu da abincin ba, balle sutura ko muhalli!
Amma idan da mace zata samu dama, sai ta ciyar da ‘ya’yanta, ta musu sutura, ta gyara jikinta. Sabanin maza da zarar sun samu alawus, aringizo ko garabasa sai su kara aure! Wani ma ya karbi bashi a banki daga nan ya kara aure, ina ruwan Malam Bahaushe.
Ciyarwa na da muhimmanci fiye da yadda ake zato, watau cin abinci bai tsaya akan ciki ya cika ba, abin ya shafi har lafiyar mutum, wanda kan kama daga uwa mai juna biyu, kai wani bayanin na nuna cewa bukatar cimaka na zagayowa, watau yara na bukata a kowane mataki, idan suka fara girma, idan sun girma, idan tsufa ya zo, domin abinci shi ne rayuwa.
Yara, idan jarirai ne, suna bukatar shayarwa kowane lokaci, bai kamata uwa ta ji ai ba ta ci abinci ba, ubangiji ya hallici mutane ta fuskar idan yaro ya tsotsi maman, nan take madara za ta zo, wato da sakon ya kai ga kwawalwar mahaifiyar. Ba yaro nono a mintinan farko bayan haihu
kan zama wani rigakafi ga cututtuka daga Mahallici.
Madarar mutane duk daya ce, da ta Turawa da Larabawa da attajirai da talakawa duk abu daya ne, tana gina yaro. Akan haka bincike ya tabbatar da cewa ko dabbobi ba su shan ruwa sai sun kai wani adadin shekaru. Haka mutane a tashin farko jarirai ba sa bukatar ruwa, sai bayan sun kai a kalla watanni shida, shi kanshi nonon na dauke da ruwa fiye da sinadarin gina jiki, kuma wajen ba su ruwan a kan sirka da wasu cuttutuka masu jawo zawo da sauransu. Sannan ba yaro nono zalla na karafafa kaifin kwakwalwar yaro, ta yadda ga lafiya, ga wayo, kuma ba za a je asibiti ba balle a nemi magani.
A lokacin da yaro ya fara wayo, ya kai shekaru biyar yana bukatar abincin dai zai gina masa jiki don ya girma yakai munzalin da zai iya noma, haka zai balaga ya zama mai jiki da jaruntar sojoji. Mata ma a matakin yara da balaga suna bukatar abincin da zai gina musu jiki, abincin nan akwai shi a karkara watau abin da ya hada da kwan zabi, zogale, gyada da sauransu.
Ma’aurata sun fi kowa bukatar cin mai kyau da kula da ‘ya’yan da suka Haifa, musamman ‘yan zamani da suka yi aure don soyayya, su suke kula da yara, sun fi damuwa da abin da ya shafi yara, wajen tarbiyya.
Lokaci ya yi da za mu bar dogara da kungiyoyin ketare da suke taimakonmu, irin su asusun kula da yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), su Sab the Children da hukumar kula da lafiyar duniya (WHO). Domin su kansu sun rage ba da gudummuwa da hidimomin da suke yi a Najeriya, sannan gwamnati ba za ta iya ci gaba da tallafawa ba ana sayen madarar tamowa (RUTF).
A haka wajibi ne ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su fito da hanyoyin. musamman a fadakar da juna game da yadda za mu kula da cimakarmu, ta hanyar ba mata da kananan yara muhimmanci don su suka fi shiga hadari idan basu sami abincin mai gina jiki ba.
Sirrin tabbatar da cewa yara sun sami kullawa shi ne tsarin shayarwa nan na shayar da jariri nono zalla a wata shidan farko (EBF), sannan a ci gaba da ba yaro nono. tare da abinci mai ruwa-ruwa da dan mulmulalle na wasu watanni daga bisani kuma a rika ba shi yana ci da kanshi, tare da yara har ya gyagije.
Manyan mutane farawa da iyaye maza da kakanni za su taka rawar gani wajen tabbatar da an ba yaro cikakkiyar kulawa, musamman idan aka hada kai da mai’aikatan kiwon lafiya, domin duk abin da suka kawo mana sun kawo don ci gaba kanmu ne, sannan a nemi taimako da addu’ar kiyayewa daga Limamai.
Akan haka ake amfani da yanar maganin cizon sauro don a ja hankalin kauyawa, domin wani ko ya karba sai ya mayar da shingen abin kariya ga lambu, ko abin shanya, shi ko magani ne, kariya ce aka baka daga zazzabi. Sai an fara gani a gidan mai gari, sai kowa ya koya!
Tabbas muhimmancin ciyarwa ya wuce duk yadda muke tunani, idan ba a kulla da mata ba alumma a dunkule za a shiga yanayi. Kula da matan zai kawo zaman lafiya da ba ‘ya’ya tarbiyyar zama masu nagarta, domin idan aka gina kwakwalwa an gama da talauci. Dole talauci ya bace, idan dan uwansa jahilci ya tsere! A nan kula da mata ya koma ma’aikatar ilimi, domin mace mai ilimi da jahila akwai bambanci, mai ilimi za ta kula da kanta, cikinta abin da ta haifa da kai kanka mai gida, jahila ko nema take a sake ta, kazanta ga ba ta iya dafa abinci ba.
Akan samu sauki idan aka bi wannan matakin, hatta a gwamnatance! Domin idan aka tabbatar da an ciyar da mutane yadda ya kamata ta hanyar agazawa manoma da karawa ‘yan kasuwa jari da bai wa dalibai tallafin karatu an samu sauyi. Kuma rashin yin haka zai samar da cututtuka su yadu, a samu annoba, gwamnatin ta nemo magani, ina asibitoci, da karancin likitoci za a ji ko rashin wadataccen magani; Ko manyan goben? watau matasa za a karafafawa lafiya, ta yadda jikinsu da kwakwalwarsu za su ginu, su zama jari ga jihohinsu da ma kasarsu.
Wasu manoman suna da kananan gonaki, babu dabbobin balle a yi kiwo, ba jari, ba sana’a. Ya rage ga gwamnatoci a kowane mataki su koya wa mata sana’o’i da jarin da ya amsa sunansa don karramasu ko zabbubuka sun zo! A ba su horon kan noman albasa da rogo da yin lambu a bayan gida. Kiwo kamar kiwon kaji da agwagwa da tattabaru da salwa. Ko a kwananan wani gwamna ya ba mata awaki a wani mataki na raya matan karkara. A saida, a ci, domin abinci shi ne rayuwa.
Buhari Daure [email protected] <[email protected]>Modoji, Katsina.