Daga dowar Najeriya karkashin tsarin dimokuraɗiyya a 1999 zuwa yanzu, Majalisar Dokokin kasar ta shekara 25 ta aiki babu katsewa, inda ta samar da dokoki sama da 800 daga kudurori da aka gabatar a gabanta.
Majalisar dattawa ta hudu (1999 2003) ta yi dokoki 65 yayin da Majalisar Wakilai ta yi 112, inda zaurukan majalisar biyu suka haɗu wajen yi dokoki 65.
An samu ci gaba sosai a majalisa ta 5 wadda ta samar da dokoki 129, amma adadin ya ragu zuwa 72 a majalisa ta shida, kafin ya kara yin sama zuwa 128 a majalisa ta 7.
Majisa ta takwas ta samar da dokoki 282 kafin daga bisani adadin ya koma 134 a majalisa ta 9.
- Kotu ta hana ’yan sanda da sojoji fitar da Sanusi daga fada
- Cushe: Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Ningi
Aminiya ta yi nazari kan wasu muhimman dokoki 10 da majalisar dokokin Najeriya ta samar.
1. Dokar Man Fetur
A watan Agustan 2021 ne tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan dokar bunƙasa harkokin man fetur (Petroleum Industry Bill) wata ɗaya bayan majalia ta amince da ita.
An shafe sama da shekara 20 ana taƙaddama da ce-ce-ku-ce ba tare da an samar da dokar ba.
Masana sun ce samar da dokar zai kawo inganci da ci gaba mai ma’ana a bangaren mai na kasar.
2. Gyara Dokar Zaɓe
Masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya sun bayyana cewa nasarar babban zaɓen 2023 na da alaƙa da gagarumar gudunmawar majalisa ta tara, wadda ta yi aikin gyaran dokar zaɓe.
A ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 ne, shugaban ƙasar na wancan lokaci ya sa hannu a kan dokar zaɓen a wani kwarya-kwaryan biki da shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilai suka halarta.
Dokar dai ta kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da zaɓe sannan ta ba da damar amfani da fasahar zamani domin tabbatar da zaɓuka masu inganci da tsafta.
3. Dokar yaƙi da ta’addanci
A watan Oktoban 2022 ne Buhari ya sanya hannu a kan dokar yaƙi da kuma haramta ta’addanci da aka yi wa gyaran fuska, da kuma dokar yaƙi da halasta kuɗaden haram.
Sabuwar dokar yaƙi da ta’addancin ta maye gurbin wata takwararta da aka yi a 2011, bayan garambawul ɗin da majalisa ta tara ta yi.
Wasu masana a lokacin sun ce dokar yaƙi da ta’addancin za ta samar da ingantaccen tsarin doka wajen ganowa da rigakafi da haramtawa da gurfanarwa gaban kotu da kuma hukunta duk wani aikin ta’addanci da ma masu samar da kuɗaɗe don aiwatar da ta’addanci da bunƙasa ta’addanci da baza miyagun makaman hallaka ɗimbin jama’a.
4. Dokar Hukumar Kula Da Almajirai
A ƙarshen mulkin Buhari ne ya sanya hannu kan dokar kafa wata hukuma da za ta kula da sha’anin almajiranci da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta don kare su daga shiga halin ni-‘’a-su da kuma ci da guminsu.
Dokar ta sha fama da matsananciyar adawa daga sassa daban-daban da kuma ƙungiyoyi a Najeriya tun bayan gabatar da ita a zauren majalisa ta tara.
Akwai miliyoyin ƙananan yara a Najeriya da ke gararamba a kan tituna ba tare da zuwa makaranta ba.
Kazalika, masu fafutuka sun shafe tsawon shekaru suna kiraye-kirayen a ɓullo da matakan kula da tsarin karatun almajiranci a ƙasar.
5. Dokar Gyaran tsarin Mulki
Bayan tafka muhawara a ranar 2 ga watan Maris ɗin 2022, majalisa ta tara ta kaɗa ƙuri’a kan wasu muhimman batutuwan da aka so yi wa gyara domin inganta tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Kudurori 68 na haɗin gwiwar ne majalisa ta tara ta kaɗa ƙuri’a a kansu.
Amma ’yan majalisar sun yi watsi da ƙudurin neman a bai wa shugabannin majalisun tarayya da cif joji-joji rigar kariya, sannan sun ƙi amincewa da bai wa mata kashi 15% na shugabancin jam’iyyu.
A gefe guda kuma majalisar ta amince da bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kai, sai dai ƙudurin bai kai labari ba a majalisun dokokin jihohi daga bisani.
6. Dokar ’Yancin Samun Bayanai
Dokar ’yancin bayanai (FOI) wata doka ce da ke goyon bayan bin ba’asin bayanai kan yadda shugabanni ke tafiyar da al’amuran mulki.
Dokar ta FOI na neman inganta dimokuraɗiyya a Najeriya ta hanyar bai wa ’yan ƙasa ’yancin samun bayanan daga ofisoshin gwamnati.
An fara gabatar da ƙudurin dokar a shekarar 1999, inda aka yi ta kai ruwa kafin daga bisani shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya sanya hannu kai a ranar 28 ga Mayu, 2011.
Dokar a hukumance, ta bai wa jama’a damar samun bayanai daga gwamnati domin sanin haƙiƙanin abin da ke tafiya a gwamnatance.
’Yan jarida, lauyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yi kai-komo don ganin wannan doka ta tabbata.
A 2021, Majalisar Wakilai ta ce cibiyoyin gwamnati 73 daga cikin 900 ne suka fara aiki da dokar wajen fitar da bayansu ga al’umma.
7. Dokar Hana Auren Jinsi
A 2014 Majalisar Dattawa ta kafa dokar da ta tanadi hukuncin ɗaurin shekaru 14 ga duk wadanda suka gudanar da aure tsakanin jinsi guda.
’Yan majalisar sun yi muhawara sosai kafin su amincewa da dokar da ta tanadi daurin da ka iya kai shekaru 14 ga masu yin auren jinsi.
Dokar har wa yau ta nadi hukuncin ɗaurin da zai iya kai wa shekaru 10 ga duk waɗanda suka shaida ko kuma suka taimaka aka ɗaura auren jinsi guda.
Dama luwaɗi ko maɗigo haramun ne a karkashin dokokin Najeriya, kuma ƙungiyoyin Musulmi da Kiristocin ƙasar sun haɗa kai wajen yin Allah wadai da dabi’ar kuma suka bayar da gagarumin goyon baya wajen kafa dokar.
Kafin a zartar da dokar dai, ƙungiyoyi da dama masu rajin kare haƙƙin bil adama sun yi ta kiraye-kirayen da kada a kafa dokar.
8. Dokar takarar Matasa
A ranar 31 ga watan Mayun 2018 tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar bai wa matasa damar tsayawa takara.
Kudirin ya bai wa matasa masu shekara 35 damar takarar shugaban kasa, ’yan shekara 25 kuma takarar majalisar wakilai.
Sai dai babu sauyi a shekarun waɗanda ke neman kujerar gwamna ko kuma Sanata – wato za su fara ne daga shekara 30 zuwa sama.
A watan Yulin 2017 ne majalisar dattawa ta amince da ƙudurin da zai bai wa matasa damar tsayawa takarar shugaban ƙasa da gwamna da majalisun dattawa da na wakilai.
Ana ganin matakin wani gagarumin ci gaba ne, kuma wasu matasan ƙasar sun nuna farin cikinsu kan sauyin da aka samu.
A baya dai mutane da dama sun nuna shakku kan ko shugaban zai amince ya sa hannu kan dokar.
9. Dokar Rancen Kudin Karatu
Shugaban Najeriya na yanzu, Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa dokar bai wa ɗaliban manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu ƙaramin ƙarfi damar samun rancen karatu mara ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu.
A watan Nuwamban 2023 ne majalisar dokoki ta amince da ƙudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar za ta riƙa bai wa ɗaliban manyan makarantun bashin kuɗin makaranta.
Dokar ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma, a cewar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo ƙudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta ƙasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana damar samun ilimi mai zurfi saboda rashin kuɗi.
Gabanin fito da wannan dokar dai, bankuna kan bayar da bashin kuɗin karatu ne ga iyayen yara wanda shi ma akwai sharuɗa da kuma taƙaitaccen lokacin biya.
Da yawan ɗalibai masu rangwamen gata kan jingine karatu mai zurfi saboda rashin kuɗi ko kuma su riƙa wasu sana’aoi ko ayyukka da ba su kamata a ce suna yi ba a lokacin da suke karatu don dai su samu abin biyan kuɗin karatun.
10. Dokar Hukumar Raya Arewa Maso Yamma
A ranar 16 ga watan Mayun da muke ciki majalisar dattawa ta amince da ƙudurin kafa hukumar raya yankin Arewa maso Yamma domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Kudurin ya zama doka ne bayan majalisar ta amince da rahoton kwamitin ayyuka na musamman a kan kafa hukumar ta NWDC.
Ana sa ran sabuwar hukumar za ta taimaka wajen ƙara kusanto da Gwamnatin Tarayya zuwa ga yankin domin biya wa mutane buƙatunsu.
Idan aka kafa hukumar, za ta taimaka wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta da ma kasar baki ɗaya.