Jarumar Kannywood Hafsat Hassan, wadda aka fi sani da Ammi, ta bayyana shigarta masanana’anar a matsayin muguwar kaddara.
Ammi wadda ta taka rawa a fina-finai irinsu Alaka, Ke Duniya, Surukan Zamani, Uwar Gulma da sauransu, ta ce ta yi da na sanin shiga Kannywood.
“Gaskiya na yi da-na-sanin shigata fim,” in ji jarumar, tana mai cewa sai da ta shiga Kannywood ta gane cewa ashe kallon kitsen rogo take wa masana’antar.
Ta bayyana cewa a rayuwarta ba ta taba ganin rashin tarbiyya ba kamar abin da gane wa kanta da ta shiga masana’ntar.
“Da muka je [location], sai in ga a daki daya za a sa maza biyu mata biyu a kan gado ana kwance.
“To a lokacin ban taba fita wani gari aiki ba, sai nake mamaki to wce irin rayuwa na kawo kaina?”
Jarumar ta ce, “A Kannywood ne wannan kujerar nan (ta mutum daya) za ku iya zama mutum uku, mata da maza.”
A cewarta, “Na taso a gidanmu da ’yan uwana maza, amma ban taba ganin na yi kusanci da maza bai sai a Kannywood,” in ji ta a hirarta da Freedom Radio.
Ta ci gaba da cewa, “Wasu kalaman sai in ji sun min nauyi in fade su, amma babu kunya tsakanin tsakanin mace da namji …abubuwan dai ba za su fadu ba.”
A jarumar, ta yi kokarin fara yi wa wasu masu yin hakan a masana’antar nasiha, amma sai suka fara yin nesa-nesa da ita.
Taurin bashin daraktoci
Ta kuma zargi abokan sana’antar tata a Kannywood da taurini bashi, inda ce saboda tsabar taurin bashinsu, sai dai a rabu da Allah Ya.
Ammi wadda ta ce ta shiga Kannywood da sana’arta ta sayar da turare da huluna ’yan Maiduguri ta ce ’yan Kannwood sun karya jarinta.
Ta ce, “Da dama sun karya ni; Mutum zai karbi kayanka sai dai ka yi Allah Ya isa.
“Idan ka yi magana, in furodusa ko darakta ne, to idan an sa ka a fim ma zai iya cire ka, komai zai iya faruwa.”
Dalilin nadamata —Ammi
Ta ce yanzu ba ta da burin da ya wuce ta yi aure, domin tsira da mutuncinta da kuma tana gudun nan gaba a yi wa ’ya’yanta gori cewa mahaifiyarsu ’yar fim ce.
Ta shawarci jarumai mata masu tasowa da “su gane cewa fim babu abin da zai ba su, kuma ba a fim ake samun kudi ba.
“Kuma su gane cewa su mata ne, kuma ko yaya kika bata lokacinki na awa daya, wallahi sai kin yi kuka na har abada kuma ba za ki gane ba sai girma ya zo miki.”
Ta kara da cewa babban abin da jarumai ke nema shi ne daukaka, “kuma daukakar ba ta Allah ake samun ta ba.”
Kalaman na Ammi dai sun dau hankali a soshiyal midiya, inda masu sharhi ke cewa ashe dai Darakta Abdallah Amdaz gaskiya ya fada a gaban Hukumar Hisba, cewa amma wasu ’yan Kannywood din suka yi masa ca.
Ammi ta ce Amdaz ya ma boye wasu abubuwan bai fada ba, saboda muninsu, domin daidai da hira tsakanin wasu maza da matan Kannywood din ta banza ta fi yawa a ciki, har ta kai ta kan ji nauyin wasu kalaman da take ji suna musaya.