✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mugunta ce ta sa Buhari kirkiro wahalar mai da canjin kudi ana dab da zabe – Gwamnan Ondo

Ya ce Buhari ya fito da matakan ne ana dab da zabe don Tinubu ya fadi

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya yi zargin da gangan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro wahalar man fetur da ta canjin kudi don yin zagon kasa ga dan takarar APC, Bola Tinubu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin Kakakinsa, Richard Olatunde, ranar Alhamis.

Ya yi zargin cewa da gangan aka kirkiro wahalhalun don kawo cikas ga shirin babban zaben ranar Asabar, da kuma musamman ga dan takarar Shugaban Kasa na APC.

Akeredolu ya kuma ce, “A gwamnatance, matsayinmu a jiya da yau sam bai canza ba. Mun amince cewa wannan batun canjin kudin da na wahalar man fetur da gangan aka kirkire su saboda mugunta, don a fausata ’yan Najeriya, sannan kuma a kawo cikas ga babban zaben kasar na 2023.

“Mun san da gangan aka yi hakan ana dab da zabe don yin zagon kasa ga jam’iyyarmu ta APC saboda ta fadi zabe a matakin tarayya da jihohi,” in ji Gwamnan a cikin wani jawabinsa da aka watsa a kafafen yada labaran Jihar.

Ya kuma yi zargin cewa Buhari ya fito da matakan ne domin dakile yunkurin mayar da mulki zuywa Kudancin Najeriya kamar yadda yake a tsarin karba-karbar da kasar ta amince da shi.

Sai dai ya ce yin hakan zai taimaka wajen rura wutar kiyayya a kasar sannan zai hafar da wani tarnaki ga tsarin siyasarta.

Kalaman na Gwamnan na zuwa ne yayin da ya rage kasa da sa’o’i uku kafin zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisar tarayya da za a yi ranar Asabar mai zuwa, 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai tuni Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sha nanata cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaben cikin nasara.

A zaben dai, Tinubu zai fafata da saura ’yan takara irinsu Atiku Abubakar na PDP da Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na LP da ma wasu da dama.