✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Yaro biya ake yi?

Sai aka amsa masa cewa Naira biyar ake biya.

Wani tsoho ne ya je birni sai fisari ya kama shi, ya ce: “Don Allah ina ake yin fisari?”

Sai aka nuna masa. Har ya yi fisarin ya tafi sai mai gidan wanka ya ce masa: “Baba ba ka ba da kudin fisarin ba.”

Ya ce: “Yaro biya ake yi?”

Sai aka amsa wa tsohon nan da cewa Naira biyar ake biya.

Har ya biya ya tafi sai kuma ya dawo, ya ce: “Yaro ai kuwa har tusa na yi, nawa ne ita kuma ake biya?”

Daga Zuladaini Gama Kano 08036667456