✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Kinayar Bahadejen da talauci ya yi wa katutu

Ba ku lura da wurin da na suma ba.

Wani Bahadeje ne talauci ya kama shi, ya rasa abin da zai yi ya samu kudi, sai dabara ta zo masa.

Sai da ya bari an biya ma’aikatan gwamnati albashi a Hadeja, sai ya tafi banki, ya samu wurin na’urar ATM an cika makil ana ta hada-hadar cirar kudi.

Bahadeje kawai sai ya baje a kasa, ya yi kamar ya suma, kumfa na fita daga bakinsa.

Nan fa mutane suka yo kansa domin taimakonsa, cikinsu sai wani ya rika cewa: “Ku samo ruwa a zuba masa domin ya farfado!”

Jin za a kwara masa ruwa sai Bahadeje ya make murya ya ce: “Ku kyale wancan wawan mai batun samo ruwa, idan da agajin ruwa nake so ai bakin Gidan Ruwa zan suma.

“Ba ku lura da wurin da na suma (banki) ba?

“Ku agaza da abin da ya dace kawai amma ba da ruwa ba!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011)