Babbar Kotun Tarayya ta hana Babban Bankin Nijeriya (CBN) sakin kudaden wata-wata daga asusun tarayya ga Gwamnatin Jihar Ribas.
A ranar Laraba ne kotun da ke zamanta Abuja ta ba da umarnin ga CBN da Babban Akanta na Tarayya (AGF) da kuma bankunan da gwamnatin Jihar take amfani da su.
Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta kotun ta kuma umarnci CBN da AGF da bankunan Zenith da Access kada su sake barin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar ya taba ko sisi daga asusun hadaka na tarayya.
Alkalin ta bayyana cewa kudaden wata-wata da aka ba wa Gwamnatin Fubara saba doka ne, kuma wajibi ne a dakatar da hakan.
- An kama dan kasar waje kan sace fitilun kan titi a Abuja
- Yadda ’yan ta’adda suka addabi babban layin lantarkin Arewa
Ta bayyana cewa gabatar da kasafin kudin jihar da Gwamna Fubara ya yi a gaban mutum hudu kacal a zauren majalisar dokokin jihar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Don haka ta kara da cewa, aiwatar da haramtaccen kasafin kudin da gwamnan ya yi ya saba tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya yi rantsuwa cewa zai kare.