✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Gajere ba yaro ba!

Aka ce na duk wanda ya doke yaron ne. Nan ya tube ya shiga fili.

Wani Bafulatani ne ya je kallon dambe, ya ga wani dan karamin yaro ya fito fili yana kirari, ana ta zubar masa da kudi, amma an rasa wanda zai tunkare shi.

Sai ya tambayi cewa: “Wannan kudin na wane ne?”

Aka ce na duk wanda ya doke yaron ne. Nan ya tube ya shiga fili.

Yaron nan ya same shi ya yi masa kwaf daya, sai ga shi kwance a kasa.

Bayan ya farfado sai ya ce: “Wannan yaron ba mutum ba ne, aljan ne!”

Daga Alhaji Danladi Chaina Kano