✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Kada ka kade takwarar mamanka! Wani mutum ne suna tafiya da matarsa a mota sai ta bata masa rai, budar bakinsa sai ya ce dama…

Kada ka kade takwarar mamanka!

Wani mutum ne suna tafiya da matarsa a mota sai ta bata masa rai, budar bakinsa sai ya ce dama mata duk jakuna ne. Ita kuma sai ta yi shiru kamar ba ta ji ba. Can za su sha kwana sai ga wata jaka a gabansu za ta tsallake titi, sai matar ta ce maigida bi a hankali kada ka kade takwarar mamanka!

 

An nuna min wanda ya tura ni!

Wani Sarki ne ya sa gasa cewa duk wanda ya shiga babban kogin garinsa ya yi wanka zai auri ’yar Sarki, ko a ba shi kudi ko rabin gari, saboda a cikin kogin akwai kadoji da dorinar ruwa da sauransu.

Ranar gasar ana tsaye cirko-cirko an rasa wanda zai fada, kawai sai aka ji tunjum! Ana dubawa sai aka ga wani dan Fulani yana bunjum-bunjum a kogi. Yana fitowa aka yi ihu ana tafi. Shi kuma kai-tsaye sai ya tafi wurin Sarki. Sarki ya ce: “Me kake so ’ya ta? Dan Fulani ya ce, “A’a!” Sarki ya ce kudi? Dan Fulani ya ce “A’a! Sarki ya ce ko rabin gari? Dan Fulani ya ce “A’a.” Sarki ya ce to me kake so? Sai Dan Fulani ya ce so nake a nuna min wanda ya tura ni, in shi ubanshi!

Daga Daga 09092969381

 

Oga Alkali mun zauna mishi!

Wani Ibo ne ya je kotu ya iske ana shari’ar wata mace kan zamba, inda aka yanke mata hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu 250.

Sai Alkali ya ce za a tafi da matar gidan kaso amma idan akwai wanda zai tsaya mata, to za ta iya samun ’yanci.

Ibo ya duba ya ga babu wanda ya tsaya wa matar, sai ya ce a ransa “Hausa mugu ne wallayi, zai bari wannan mutum ya yi cekala biyar a prison saboda tsayawa!”

Sai ya mike tsaye ya ce “Alkali, mun saya mishi.”

Alkali ya ce to, tunda an samu wanda zai tsaya mata ba za a kai ta gidan kaso ba. Alkali ya tambayi Ibo sunansa, ya ce “Mu ne Chinedu.”

Alkali ya ce to, za ka biya tarar Naira dubu 250 domin wannan mata ta samu ’yanci tunda ka tsaya mata.

Chinedu ya ce “Meni ne?”

Alkali ya ce Naira dubu 250.

Sai Chinedu ya ce “Oga Alkali, mun zauna mishi… (wato ya fasa tsaya mata) kai mun kwanta mishi.”

Daga Alhaji Umar Foreber Gashua

[email protected]