Sarkin Fawa
Wani Sarkin Fawa ne aka kai shi kara kotu, sai alkalin ya yanke masa hukuncin daurin wata shida. Sai Alkali ya ga bakin Sarkin Fawa yana motsi kamar yana fadin wani abu a boye. Alkali ya ce masa: “Ba zagina ka yi ba dai ko?” Sai Sarkin Fawa ya amsa da cewa: “Amma kuma ai ba yabonka na yi ba!”
Ardon Fulani
Wani Ardon Fulani ne ya yi tafiya sai ya ba da rikon gari, lokacin da ya dawo sai jama’arsa suka zo yi masa sannu da zuwa.Sai wani ya ce: “Yallabai da ka tafi sai muka ji dadi.” Ardo ya ce: “Da na dawo fa?” Sai mutumin ya ce: “Sai muka kara jin dadi!”
Labarai daga Rabi’u Yunus Kura, Agege-Legas 08035788242
Kafarka, kafata
Wani Bakabe ne ya kawo wa matarsa cefane babu magi sai ya ce mata: “Ki karbi magi a wurin makwabcinmu mai shago. Koda dare ya yi ya dawo daga aiki sai ya ce a kawo masa abinci, sai aka kawo masa danyen abinci. Ya ce: “Yaya haka?” Sai ta ce: “Ba magi.” Sai ya tashi tsaye ya ce mata: “Bari in je in sayo.” Da ya fita bai dawo ba sai bayan mako uku. Ya dawo da asuba dauke da magi katan guda. Matar ta ce: “Maigida ina ka shiga?” Ya ce: “Magin ne ya yi wahala.” Can kuma sai ya ce mata: “Ke na manta kayana a mota.” Sai ta rike shi, ta ce: “Ai wallahi kafarka kafata, duk inda za ka!”
Daga Haruna Duniya Boy Legas, 08033538654
Bari in gani
Wani mutum ne ya sayo jaridar Aminiya yana karantawa sai wani ya zo wajensa ya ce masa da Ingilishi “Let me see.” (Bari in gani). Shi kuwa ya harde kafa, ya dora daya a kan daya, da gadara ya ce masa: “Ba let me see ba ne, Aminiya ce, na bar let me see din a gida.” Wai shi ya dauka let me see sunan wata jarida ce.
Daga Ibn Umar Bauchi, 07066777864.