Wani Alhaji
Wani Danfulani ne ya je Makka ya dawo, sai abokansa suka zo suna yi masa barka da zuwa. To daya daga cikinsu sai ya kira shi da sunansa ba tare ya ce masa Alhaji ba, sai daya daga cikinsu ya ce: “Ba za ka kira shi da Alhaji ba? Sai Alhajin ya ce: “Rabu da shi, rabu da shi, iya alhakin da mala’iku suka rubuta masa ya ishe shi!”
Daga Isma’il Adamu Manzo Kiyawa.
Kashako
Wani Bafullatani ne ya hau mota daga Kano zuwa wani kauye. Ana cikin tafiya sai yaron mota ya ambaye shi inda zai sauka. Sai ya ce ya mance sunan garin. To a cikin motar akwai wani mai manyan hakora zako-zako. Da Bafulatani ya gan shi, sai ya ce: “Wallahi sunan garin kamar hakora wancan!” Yaron mota ya ce ko: “Kacako?” Bafulatani ya ce: “Gaskiyarka kare, Kashako!”
Daga Sadik Dahiru Rafindadi Katsina, 08141993458
Dan Jigawa
Wani mutumin Jigawa ne ya je wajen intabiyu, don a dauke shi aiki kuma an sanar da shi cewa da Ingilishi ake gudanar da ita. Shi kuma ya dauka komai aka tambaye shi da Ingilsihi zai amsa. Ga yadda intabiyun ta kasance:
Malami: What is your name? (Yaya sunanka)?
Dan Jigawa: New 10 Kobo (Sabo Sule).
Malami: From which LGA? (Daga wace Karamar Hukuma)?
Dan Jigawa: From Stone LGA (Dutse LGA).
Malami: What is the work of your father? (Me ke sana’ar babanka)?
Dan Jigawa: Motor Dog (Karen Mota).
Malami: Which kind of motor? (Wace irin mota yake tukawa)?
Dan Jigawa: Dismiss the Hyena (A Kori Kura).
Wakar yaro
Wani yaro ne dan makaranta, kullun direbansa idan ya je dauko shi a makaranta sai ya fara rera waka, yana cewa: “Idan babana sarki ne, babata ta zama sarauniya, ni kuma dole a ce min yarima. Idan kuma babana zakara ne, mamata kuma kaza, ni kuma na zama dan tsako.” Ashe direban nan ya fusata sai ya ce wa yaron nan: “Idan kuma babanka barawo ne, mamarka kuma ashawo, kai kuma me za ka zama?” Sai yaron nan ya ce: “Sai in zama direba!” Tun daga nan bai sake yin wata magana ba har suka isa gida.
Daga Danladi China 08034463170