✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Tun a farkon yakin aka kashe ni! Wata rana a makaranta sai malamin su Shehu Jaha ya shiga aji domin yi wa dalibai jarrabawa, malamin…

Tun a farkon yakin aka kashe ni!

Wata rana a makaranta sai malamin su Shehu Jaha ya shiga aji domin yi wa dalibai jarrabawa, malamin ya tambaye su cewa: “Ka dauka kai soja ne da kuka dawo daga filin yaki, rubuta abubuwan da suka faru a lokacin da kuke filin daga.” Malamin sai ya fara tattara takardun dalibai, sai ya ga takardar Shehu Jaha bai rubuta komai ba; sai ya tambaye shi dalilin da ya sa bai rubuta komai ba. Shehu ya amsa da cewa: “Ai tun a farkon yakin aka kashe ni!”

Maganin mutuwa

Wani yaro ne ya ce da malaminsa wai ya fada masa maganin mutuwa. Malamin sai ya gaya masa cewa: “Ka karanta A.B.C.D har zuwa Z kafa dubu daya, ka tofa a ruwa ka shanye kuma ka shafe jikinka da shi. Idan ka yi haka wallahi ba za ka mutu ba sai ranar da kwananka ya kare.”

Labarai daga Haiman Khan Ra’is, 08185819176

Kukan kauna

Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya fita sai ya duba aljihunsa, ya ga Naira 50 kadai yake da ita. Sai ya ce wa mai nama: “Ka ba ni nama na Naira 50 amma ka yanka mini albasa da yawa.” Aka yanka masa ya kawo mata, dama an dauke wuta, akwai duhu. Sai ya tura mata naman, shi kuma ya kama cin albasa. Nan fa idanunsa suka tara hawaye. Can aka kawo wuta, lokacin sun gama cinye nama. Yarinya ta ga idon saurayinta na zubar da hawaye, ta tambaye shi dalilin da yake kuka. Sai ya ce: “Tsananin kaunarki ce ta sanya ni kuka!”

Mahaukacin Babarbare

Wani Babarbare ne aka kai shi asibitin mahaukata don a duba lafiyarsa ko ya warke. Da suka je sai ya kama wata bishiyar mangoro ya hau, tunda safe. Aka yi, aka yi ya sauko ya ki sai da yamma sai ya fado kasa tik. Likitocin suka tambaye shi cewa: “Ma ya sa ka fado kasa?” Sai ya ce: “Nuna na yi, shi ya sa na fado.”

Labarai daga Dan Fagge, 08058009561

Kunna talabijin

Wani Bafulatani ne ya je birni sai ya ga talabijin kuma ya burge shi. Domin ya burge ’yan uwansa a kauye sai ya saya. Mai kanti ya ce masa: “Ai da ka je gida ka hada mata wuta, ka kunna sai kallo kawai!” Bafulatani cikin sauri ya dauki akwatin talabijin, yana zuwa gida sai ya tattara karmami ya rufe talabijin, ya banka masa wuta. Ya koma gefe daya yana kallon ikon Allah.

Daga Nafisa Basiru Sadi, 07037902893