Alhaji Aliko Mohammed (Dan Iyan Misau) daya ne daga cikin mutane na farko na kwararrun akantoci daga Arewa.
Ya shafe kusan dukkan rayuwarsa a aikin kamfanoni, inda ya shugabanci kamfanoni da dama ciki har da NICON Insurance da Kamfanin Buga Jaridu na Daily Times da Bankin Arewa.
A karshe ya zama Shugaban Kasuwar Hada-Hadar Hannayen Jari ta Najeriya, kasuwar da ke kula da harkokin kamfanonin kasuwar hannayen jari a Najeriya.
A matsayinsa na Shugaban Kare Muradun Arewa (ACF), sau da dama yakan jagoranci yunkurin nema wa yankin hanyoyin fitar da shi daga kangin da yake ciki.
A tattaunawarsa da gidan talabijin na Trustu TV ya yi tsokaci kan rayuwarsa da karatunsa da sauran batutuwa:
Kamar daga farko ba ka yi niyyar shiga harkar hadahadar kudi ba saboda bayan ka kammala Makarantar Midil Bauchi ka wuce Makarantar Koyar da Tsabta da ke Kano. Shin haka batun yake?
A wancan lokacin Sarkinku ne yake yanke shawarar ko ina mutum zai je. A lokacin mu hudu ne muka kammala karatu a Midil, sai ya ce dayanmu daga gidan sarauta ya kamata ya zama akawu domin ya yi aiki a Majalisar Sarki.
Dan uwana kuma ya tafi Makarantar Nazarin Larabci saboda asalin zuriyarmu limamai ne.
Fiye da shekara 200, gidanmu ke rike da limanci a Misau, don haka a shirye yake ya shiga makarantar. Musa ya zama malami.
Su ne suke zaba mana, inda za mu je sai dai kawai a ce maka tafi can.
Lokacin da na shiga makarantar koyar da tsabta mukan yi jarrabawa duk bayan wata shida.
Domin nuna cewa zan iya, na zauna a can na wata shida, na samu nasarar cin jarrabawa, inda na zo na biyu; sai na sanar musu cewa zan bar makarantar, inda na koma UAC.
A wancan lokacin kusan kowa na neman fara aikin gwamnati ne. Me ya sa ka yanke shawarar tafiya UAC?
A wancan lokacin a gaskiya UAC na jan hankalin matasa daga Arewa.
A lokacin ba su jima da kammala ginin hedkwatarsu a Kano da suke kira Gidan Golde.
Aiki a wajen yana da kyau a lokacin, kuma albashinsu ma ya fi na gwamnati yawa. Shi ya sa na je can.
Ta yaya ka samu damar zuwa Ingila don karatun kwarewa a aikin akanta?
Daga UAC ne aka tura ni zuwa kananan rassansu. Na yi shekara biyu a Ringim, sannan na gane cewa zan so in yi aikin gwamnati, sai na nemi takardar neman aiki aka tura ni sashen Baitulmali.
A lokacin ana kiran Ma’aikatar Kudi da Baitulmali.
Baitulmalin Jihar Arewa ke nan?
Eh, Baitulmalin Jihar Arewa. A can Kaduna na yi shekara uku, sannan na bar su na tafi Bankin Backlays.
Sun kasance suna daukar ’yan Arewa aiki, kuma albashinsu yana da kauri. Daga nan ne na je Kamfanin Gaskiya Corporation a matsayin Mataimakin Akanta.
Gaskiya Corporation ya tura ni zuwa kasar Birtaniya domin samun kwarewa a harkar akanta, tare da alkawarin cewa idan na dawo zan karbi mukamin daga hannun babban akanta kuma sakataren kamfanin wanda kwara ne.
Harkar akanta tana da tarihin kasancewa mai wahalar sha’anin karatu. Yaya ka samu ka cim ma nasara?
A lokacin ina makaranta, darasin lissafi shi ne wanda na fi kwarewa a kai kuma na fi so.
Karatun akanta ba ya da wahala, bai ma kai karanta aikin injiniyanci wahala ba, kawai mutum zai yi ta amfani ne da lambobi.
Mutum yana aiki da kudi kuma galibi mutane suna gudun wadannan abubuwa.
Mutum nawa ne kwararrun akantoci kamar kai suke a wajen a lokacin?
Babu ko daya. Lokacin da na zama kwararren akanta, marigayi Wazirin Katsina Hamza Zayyad ne kadai a wannan fanni.
Hakan ya sa ka zama na biyu a Arewacin Najeriya ke nan. Kai ne mai kula da harkokin kudi na kamfanoni da dama a Arewa kamar Kamfanin NNDC da NNIL.
Wadannan kamfanoni da alama sun taka muhimmiyar rawa a baya, sai dai ko sun ruguje gaba daya ko suna tangal-tangal.
Me ya sa hakan ya faru?
Lallai gwamnatin Arewa a karkashin marigayi Sardauna tana da matukar sha’awar bunkasa yankin.
Sun kafa Hukumar Raya Arewa, wadda ita ce farkon Kamfanin NNDC. Daga baya suka hada kai da gwamnatin Birtaniya suka kafa Kamfanin NNIL.
Na yi aiki da su duka. Kamfanin NNIL na zuba jari ne kawai. Sun karbe jarin da NNDC ya yi da baki da sauransu.
Kuma sun kasance suna taka muhimmiyar rawa sosai sa’annan suna biyan ribar jari na kashi 50 cikin 100 duk shekara. Kasuwanci ne mai kyau sosai.
To amma me ya sa wadannan kamfanoni suka durkushe. Shin me ya faru?
An kafa NNDC ne domin yin wannan aiki. Sun zo da jari daga baki ’yan kasashen waje.
Abin bakin ciki shi ne, baki ba sa zuwa kasar nan domin zuba jari.
A koma yaya ne, suna kuma bukatar kudi mai yawa don zuba jari, kai kanka ka san da haka.
Ita kanta gwamnatin ba ta da isassun kudin da za ta zuba jari; don haka kamfanonin ba sa kawo kudade. Shi ya sa abin ya faskara.
A matsayinka na daya daga cikin kwararrun akantocinmu da ya kasance mai kula da harkokin kudi na wadannan kamfanoni na Arewa, me ya sa Arewa ke fuskantar kalubale wajen gudanar da kasuwanci?
To, daya daga cikin manyan dalilan a ganina, shi ne tarihinmu ko tushenmu.
A Arewa ba ma fahimtar kasuwanci, ba mu san saye da sayarwa ba, baya ga mutanen Kano da wani karamin sashen Katsina.
Yawancinmu ba mu san komai ba game da kasuwanci, saboda haka ba mu tafiyar da shi yadda ya kamata. Sakamakon haka muke tafka hasara, wadda za ta sa kowane kasuwanci ya ruguje.
Wadanne harkokin kasuwanci ne kuka tafiyar kuma mene ne darussan da aka samu daga hakan?
Alal hakika, Kamfanin NNDC ya yi wa kasar nan abubuwa da dama.
Sun hada kai da baki (Turawan Ingila) sun samar da masaku hudu, ciki har da Masakar Kaduna. Mutanen Japan da China ma sun zo.
Sun kuma samu wani dan kasuwa daga Pakistan. Akwai Masakar Arewa. Wadannan sun yi nasara sosai a lokacin.
Kuma sun kasance suna samar da kaso mai yawa na riba ga Kamfanin NNDC, wanda yake haskakawa sosai.
Kwatsam da suka fice babu wanda ya rage kuma kamfanin ya zama abin da ya zama a yanzu.
Wadanne matsaloli ka fuskanta a yayin gudanar da kasuwancinka na kashin kanka, idan ka yi hakan?
Ina gudanar da harkokin kasuwanci. Ka gani ko, mutane suna tunanin cewa kasuwanci shi ne saka kudi kawai, amma abu mafi muhimmanci shi ne gudanarwa.
Dole ne mutum ya tabbatar yana yin abin da ya dace da kuma samar wa kasuwa abin da take bukata, don haka idan ka samu kudi sai ka kashe wasu ka ajiye wasu.
Amma mu nan yadda muka saba ba ma yin wannan.
Lokacin da muka samu kudi muna tunanin dole ne ka kashe su. Hakika wannan ita ce matsalarmu.
Wadanne harkokin kasuwanci ka gudanar kuma wane darasi ka koya? Me za ka iya fada mana game da kalubalen hakan?
Da farko, ba mu yi imani da kayan da aka hada ko aka kera a Najeriya ba.
Mun gwammace mu je mu sayo daga kasashen waje da Dala da Fam da Yen ko wani kudi na daban.
Kuma dole ne mu samar wa kanmu kudaden nan, idan ba mu samar ba, gwamnati ce ke samar da su ta hanyar sayar da man fetur kuma dole ne mu karbi kudaden waje domin yin haka.
A gaskiya, babbar matsalar ita ce muna son sayen kayan waje. Misali, idan akwai sabuwar mota, a ce Marsandi ko makamanciyarta, sabuwarta (da ba ta wuce zuwa wata shida ba) za ka gan ta a Najeriya. Idan ba mu sayi kayanmu ba, wa zai saya?
Shin ko ka taba hada wasu kayayyaki a Najeriya kuma ka sha wahala wajen sayar da su?
Shaddar da muke sawa daga waje ake shigo da ita, amma muna da masaku.
Kodayake ba iri daya suke yi ba, amma ’yan Najeriya ba su sayenta.
Wace shawara kake da ita ga matasa masu son fara harkokin kasuwanci, musamman yadda mutane da yawa ke cewa kada su tsaya jiran aikin gwamnati?
Najeriya ta yi sa’a sosai da take da yawan jama’a da kuma arziki.
Idan ’yan Najeriya za su sayi kayan da aka yi a kasarsu da ba za a samu matsala ko kadan ba, amma ban sani ba ko saboda tushenmu ne ya sa suka fi son sayen abubuwan da aka kera a waje.
Muna son farawa daga sama amma kada ku damu da yadda za mu kai ga wajen.
Ka shugabanci kamfanoni da dama kuma a karshe ka jagoranci Hukumar Kula da Hadar-Hadar Hannayen Jari. Ta yaya hakan ya faru? Ta yaya ka shiga duniyar kamfanoni ta Legas?
An nada ni Shugaban Hukumar Inshora ta NICON a lokacin ina tsakanin shekara 32 zuwa 33.
Daga nan na shiga Kasuwar Hada-Hadar Hannayen Jari ta Najeriya na zama mamban hukumar tun ina da kananan shekaru. Daga nan, cikin sauki sai likkafa ta yi ta jan gaba.
Bankin Arewa fa?
Na yi Shugaban Bankin Arewa na tsawon shekara 10.
Kamar yadda ka sani, a wancan lokaci bankin na jihohin Arewa 10 ne, amma yanzu jihohi 19 ne.
Ni mamba ne a hukumar kasuwanci, sai suka zabe ni a matsayin darakta a bankin.
Marigayi Waziri Ibrahim shi ne Shugaba.
Da aka soma siyasa ya fita ya kafa jam’iyyar siyasa, sai aka nada ni Shugaban Bankin.
Wani nadi da ya bai wa mutane da yawa mamaki shi ne na jaridar Daily Times. An nada ka Shugaban Kamfanin, duk da kasancewarka kwararren akanta, kuma nadin ya zo ne a ranar da Adamu Ciroma ya zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN). Jama’a sun dauka cewa an yi kuskure ne a wajen nadin, kai ake sa ran za ka je CBN shi kuma Ciroma ya tafi Daily Times. Yaya za ka warware mana zare da abawa?
Ban san mene ne tunanin Shugaban Kasa Murtala Mohammed na lokacin ba.
A gaskiya na yi tunanin wurin da zan je shi ne CBN, amma sai ya ce in je gidan jarida, inda Adamu Ciroma ya shafe lokaci yana aiki.
Da farko dai ya karanci tarihi a jami’a kuma aka nada shi Gwamnan Babban Bankin Kasa.
Ba ya iya ko karanta takardar bayanan kadarorin kamfani. Ina tsammanin saboda sanin cewa ba zai iya ba, kawai sai ya ajiye aikin bayan shekara daya.
Wadansu mutane sun tambayi Shugaban Kasar inda ya ce, “ya kamata dukkansu biyu su je su samu kwarewa.”
Ban san dalilinsa na yin haka ba, amma na yi farin ciki da na je wurin domin ya bude min ido kasancewata dan Najeriya. Ina tsammanin na koyi abubuwa da yawa a can.
A matsayinka na kwararren akanta wanda ya samu kansa a kafar yada labarai, shin aikin ya yi maka wahala?
Ni ne Shugaban Hukumar. Jaridar tana da Manajan Edita da Edita da sauransu.
Amma ba da jimawa ba da fara aikina a can sai aka samu hatsaniya, inda suka kori Manajan Darakta suka nada wani.
Ni sabo ne shi ma sabo ne. Kodayake mun samu matsala, abubuwa sun daidaita daga bisani. Na yi shekara shida a can.
Kai ne shugaban kwamitin da aka kafa domin farfado da Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian a shekarun baya. Har yanzu ba a farfado da kamfanin ba. Me ya faru?
A gaskiya a lokacin da Marigayi Shugaba Umaru ’Yar’aduwa yake Gwamnan Jihar Katsina sun nada ni domin duba lamarin.
Mun rubuta rahoto mun ba da shawarar cewa Hukumar NNDC ta dauki kusan kashi 30, ita kuma gwamnati ta tafi da kashi 70 cikin 100 domin kamfanin ya dubi lamarin ta fuskar kasuwanci yayin da gwamnati za ta samu wakilanta, amma daga karshe gwamnonin sun yanke shawarar yin abin da suke so.
Wane hali ne Kamfanin New Nigerian yake ciki?
Mun rubuta rahoto mun bai wa Gwamnan kuma ya tattauna rahoton da takwarorinsa, amma ba su dawo suka fada mana ko mene ne shawararsu ta karshe a kai ba.
Ina ganin ba ni da sha’awar gano halin da yake ciki.
Kana daya daga cikin ’yan kalilan a zamaninku da suka kwashe lokaci mai tsawo a shugabancin kamfanoni na duniya da kuma bankuna. Shin ka samu kudi masu yawa a aikin?
Ba ka samun kudi don kawai ka kasance a cikin kwamitin gudanarwa.
Da farko dai akwai ka’ida cewa ba za ku iya rancen kudi daga bankin da kuke jagoranta ba sai kun bayar da kashi 105 cikin 100 na kadara.
Yanzu ne shugaban banki zai iya cin bashin biliyoyin Naira, a zamaninmu ba za ka iya yin hakan ba. Ana bin dokoki yadda ya kamata, amma ba haka lamarin yake ba a yanzu. Ban san abin da ke faruwa ba.
Bayan duk shekarun da ka kwashe a cikin kamfanonin duniya. Me kake yi yanzu bayan ritayarka?
Na yi ritaya.
To me kake yi yanzu bayan ka yi ritaya shekaru da dama?
Ba na yin komai a zahiri. Kullum ina gida. Idan ka gan ni na fita yanzu, ranar Juma’a ce zan je masallaci ko wani muhimmin dalili, in ba haka ba, ba na yin komai.
Yaya kake tafiyar da wuninka?
A cikin shekara 38 zuwa 40 da suka wuce, ina karatun Alkur’ani. Duk kwana 24 zan karanta Alkur’ani duka in maimaita shi. Abin da nake yi ke nan kullum – izu biyu da rabi da safe da daya da rana da izu biyu da rabi da yamma.
Don haka, ina bata lokacina mai yawa kan hakan kuma ina farin ciki sosai.
Yaya batun abubuwan da kake sha’awa na debe kewa?
Babu ko daya. Ina da shekara 86 yanzu.
Mutane na cewa tsofaffi ya kamata a ce suna motsa jiki sannan su rika kula da irin abincin da suke ci. Cikinsu wanne kake yi?
Akwai wani aminina wanda likita ne, sunansa Bello, ya ba ni shawarar cewa a kowace safiya ya kamata in rika zagaya harabar gidana da dakina kamar sau 20.
Ina kuma bin shawarar yadda ya dace. Ko yau din nan ma sai da na zaga.
Ina ga abinci kuma, ko kana takaita wa kanka wani nau’in? Da akwai abincin da kake ci domin kara maka lafiya ko dai kawai kana yin abin da ya zo maka haka a lokacin?
An bukaci in daina cin naman shanu, don haka nake cin kifi da kaji.
Amma kuma bayan wannan ba wani nau’in abincin da aka hana ni ci.
Ina tunawa wani lokaci ka taba cewa kana sha’awar cin yankakken burodi da kwai. Shin abinci ne da kake ci a kullum?
Eh, har yanzu nakan ci yankakken burodi kullum a matsayin kalacin safe, amma ba wai irin na musamman din ba.
A shekarunka 86, har yanzu hannunka da muryarka suna nan daram da karfinsu.
Wani zai yi tunanin lallai da akwai wani sirri tattare da kai da ya kamata ka karar mana domin mu zama cikin koshin lafiya.
Wannan baiwa ce daga Allah, kuma wani abin mutum ba zai ma iya fayyace shi ba.
Kuma bayan zagayen harabar gidana da na fada maka, ba wani abu na daban da nake yi.
Ko kana noma, wanda shi ma daya ne daga cikin ayyukan mutanen da suka yi ritaya?
A’a. Ina da gonaki sai dai a halin yanzu na daina noma. Babbar gonata tana Masarautar Misau.
Wa yake kula da gonar?
’Ya’yana da ’ya’yan ’yan uwana da makamantansu.
Batun iyali, kamar dai matarka daya ce da yara. Shin haka batun yake?
Ina da yara takwas, guda namiji ne sauran kuma mata ne.
Sai dai abin farin ciki a nan, dukkansu kwararru ne a fannonin aiki daban-daban.
Babbar ’yata likita ce. Sannan ita ce Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna.
Gabanin nada ta, tana aiki ne da Majalisar Dinkin Duniya. Ta yi digirinta a can.
Sai dai Gwamnatin Jihar Kaduna ba za ta iya biyan ta albashi da Dala ba, ala tilas ta sadaukar.
Alal hakika, abin jin dadi ne mutum ya sadaukar da wannan.
Wato kwamishina ce a Jihar Kaduna ko Gombe?
Kwamishinar lafiya ce a Jihar Kaduna.
Na yi zaton kai dan Jihar Gombe ne?
A’a, ni dan Misau ne a Jihar Bauchi.
Kai mutum ne da ya kewaya duniya sosai. Wadanne kasashen ne suka fi ba ka sha’awa?
A matsayina na dan Najeriya, a kowane lokaci Birtaniya ce kasar da ta fi ba ni sha’awa musamman ga ire-irenmu da muka yi karatu a can.
Sannan mutum zai iya zama a oteotel mafiya inganci.
Haka kuma, ina da abokai da harkokin kasuwanci sosai a Jamus ma, don haka Jamus ita ma tana daga cikin kasashen da nake sha’awa.
Ba na zuwa Amurka. A cikin shekara 60 da suka gabata sau daya kawai na ziyarci Amurka.
To a Nahiyar Afirka fa?
A Afirka na sha ziyartar kasar Masar.
Nakan je Ghana ita ma a-kaia-kai saboda akwai wani kamfanin mai wanda nake shugabanta kuma hedkwatarsa tana birnin Accra.
Hakan ya sa a duk lokacin da muke da zaman masu ruwa-da-tsaki na kamfanin, can muke haduwa domin zaman. Sa’annan sau tari na ziyarci Nijar.
Har yanzu ban ji ka ambaci ayyukan da kake gudanarwa a gefe ba. Ka zama Shugaban Kungiyar Kare Muradun Arewa, (ACF) bayan da ka yi ritaya. Yaya ka samu kanka a wannan…?
Akwai dattijan Arewa a ciki inda marigayi Abdurrahman Okene ya zama shugaba, ni kuma Mataimakinsa.
Shi ma Wazirin Katagum ya jagoranci wani sashen, sun kai kamar su uku.
Marigayi Sarkin Musulmi Maccido ya ba da shawarar mu hadu a inuwa guda, sannan ya ce mu sanya sunan Arewa Consultatibe Forum.
Ni na fara shugabanci. Kamar yadda ka sani muna karba-karba tsakanin shiyyoyi uku na yankin.
Na fara da rike Ma’ajin Kungiyar, inda aka bai wa yankin Arewa maso Gabas kujerar Shugaban Kungiyar.
A lokacin da aka kai shugabancin Arewa maso Gabas, shekara uku kawai na yi saboda na karbi jagorancin ne daga wani mutumin yankin, Manjo-Janar (IBM) Haruna.
Cikin tsawon shekaru Kungiyar ACF ta kasance cikin fadi-tashin hada kan Arewa sannan ta samar wa yankin alkibla. Sai dai kamar har yanzu babu ko daya daga ciki da ta cimma.
Shin kungiyar ta cancanci tunkarar lamuran nan kuwa?
Abin mamaki ne wai mutane su fito su ce Arewa kanta ba a hade yake ba.
Idan ka duba yankin Gabas (na Ibo) yare guda ne su, haka ma yankin Yamma kabila daya ce, amma a Arewa muna da daruruwan kabilu kuma duk da haka muna zama karkashin inuwa guda. Abin mamaki ne gaskiya.
Ke nan ba ka damu da kungiyoyin da ke bangarewa kamar zauren ’yan Midil Belt, wacce ya dace a ce tana daga cikin kungiyar ta ACF?
Ko da sun kasance suna tare da mu a baya ko kuma ma har yanzu muna tare da su tsagwaron siyasa ce kawai.
Har yanzu ina da matsaloli da abin da muke kira da Kungiyar Dattawan Arewa, saboda tsarin mulkin ACF ya fayyace cewa kowane dan Arewa daga shekara 16 zai iya zama mamba.
Abokaina kamar Ango Abdullahi sun ji suna bukatar shiga siyasa.
Wannan shi ne gaskiyar lamarin abin da ya faru. Kawai sai suka fara tafiyar da abinsu ba tare da an kalubalance su ba.
Mene ne ra’ayinka game da lamuran siyasar kasar nan? Ko ka damu da ababuwan da ke faruwa kamar a Kaduna da sauran yankunan kasar nan?
A Najeriya ce kadai za ka samu jam’iyyun da aka yi wa rajista fiye da 100 a matsayin jam’iyyun siyasa.
Babu inda za ka ga irin wannan abin ko’ina a duniyar nan. Za a iya samar da jam’iyyu biyu ko uku ko kuma biyar amma ban da 100.
Duk wanda ya dan samu kudi da angizon jama’a so yake ya zama Shugaban Kasa, kawai sai ya kafa rukuni nasa.
Akwai bukatar a kalli mutanen da suka ce suna da sha’awar gudanar da kasar da kuma ganin tarihinsu da abin da suka yi a baya.
Ka yi kokarin tsayawa takarar Shugaban Kasa sau daya. Yaya abin ya kasance?
Tun da farko na gaya maka cewa na yi wata guda a siyasa.
Dalili kuwa shi ne, Babangida ya yanke shawara, ba gaira ba dalili, cewa duk ’yan siyasa kada su tsaya takara.
Bayan wata daya sai ya ce su dawo, amma na ce ba zan iya yin gogayya da abokaina kamar marigayi Adamu Ciroma ba, wanda ya samu tushe a siyasance. Na je na fada masa.
Yaya kake ganin aikin Shugaban Kasar da ke kai a yanzu?
Na farko dai ya kasance aminina na fiye da shekara 50.
Najeriya kasa ce mai matukar sarkakiya, don haka yana iya kokarinsa.
Kuma ka yarda da ni cewa wadansu a Arewa lallai ne mu kasance masu godiya ga Allah kan samun sa.
Lokacin shugaban da ya gabata, a kowace rana muna shigo da shinkafa daga waje da ta kai Naira biliyan guda.
Sannan a wancan lokacin muna samun kudaden waje kuma farashin mai yana da gwabi, mun zo lokacin da ba mu da man kansa, kai ko da man ma ba za mu iya yin haka ba.
Buhari ya karfafa tare da samar da kudaden noman shinkafa, ga shi yanzu mun wadata kanmu da ita.
Ko wannan ma kadai, ya yi wa kasar nan gagarumin aiki, saboda idan da a ce ba mu da kudaden waje da za mu canja sannan babu shinkafar, Allah ne kadai Ya san me zai faru a kasar nan.
A lokacin da ka ji mutane na korafe-korafe kan gazawar gwamnatin nan, me kake fada musu?
Mu dai a Arewa lallai ne mu gode wa mutumin nan. Ka je Sakkwato da Kebbi ka yi musu magana kan shinkafa ka gani. Suna noma shinkafar sau uku a shekara.
A halin yanzu mun wadata da shinkafar har muna tunanin fara fitar da ita zuwa kasashe makwabta.
Don haka, abin takaici ne mutane su rika fadin haka; Akwai abubuwa da dama a zahirance.
Muna tunkarar zaben badi, kwaramniyya ta yi yawa ta ko’ina game da wa ya dace ya yi takara kuma daga wane bangare. A ganinka me ya kamata mu yi domin daidata lamura?
Buhari bai wakilci yankin Arewa ba. Ya yi takara ne da sauran ’yan Najeriya, inda ya yi nasarar samun takarar jam’iyyarsa sannan daga bisani ya ci zaben.
Duk wani mahaluki daga kowane yankin Najeriya da yake son takara ya kamata ya fito ya yi yadda Buharin ya yi, ga fili ga mai doki ga dukkan ’yan Najeriya.
Bai dace mu rika cewa Shugaban Najeriya, daya daga cikin kasashen masu arziki a duniya, wai lallai sai ya fito daga wani bangare ba. Ina ganin hakan kuskure ne.
Abin ban dariya ma a nan shi ne a yanzu da ’yan kabilar Ibo suke fadi-tashin samun shugabancin kasa.
Na farko, har yanzu suna fafutikar kafa kasar Biyafara, wanda gaba daya wani lamari ne na daban ga Najeriya.
Ke nan kana cewa a yi watsi da batun karba-karbar mulki dungurumgum, kawai mu koma zabar shugabanni bisa cancanta da nagartar ’yan takara ko daga ina suka fito?
Ka ji abin da na yi amanna da shi ke nan.
Ba a zabi Sardaunan Sakkwato saboda ya fito daga Sakkwato ba, ya zama shugaba ne kawai kuma ai mun san yadda ya yi wa Arewa aiki.
Batun da ake yi a nan shi ne cewa Najeriya kasa ce mai matukar rabuwar kawuna, don haka zuwa wani lokacin ya kamata mu ci gaba da tafiya da tsarin karba-karbar domin wanzar da hadin kai kafin daga bisani mu bude lamarin ga wadanda suka cancanta kawai. Mene ne ra’ayinka?
A ganina nagarta ce za ta samar da hadin kan da ake magana.
Arewa ta fi yawan kabilu da bambance-bambance fiye da sauran yankunan kasar nan.
Ina ganin ya dace sha’anin shugabancin kasa a kowace kasa ya zama bisa cancanta ko nagarta ba wai a yi ta karbakarba daga wannan bangaren zuwa wancan ba.
Ke nan ba za ka yi mamaki ba idan a badi dan Arewa ya nuna sha’awar zama Shugaban Kasa bayan Buhari ya kammala shekara takwas dinsa?
Saboda me? Kawai a kyale ’yan Najeriya su zabi wanda suke so.
Kuma mene ne dalilin da za mu ce lallai in mulkin ya bar wannan bangaren to lallai ne ya koma daya bangaren?
Fassarar Dalhatu Liman