Ministan Tsaro na Jamhuriyar Nijar, Alkassoum Indato, ya ce motoci guda 19 da aka ce Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ba kasarsa har yanzu ba su karasa wajensu ba.
Ministan wanda ke magana da yawun Muhammadu Bazzoum Shugaban Nijar din ya ce, su dai har yanzu ba su ga mota ko daya daga cikin motocin ba.
- Ma’aikatan wutar lantarki sun janye yajin aikin da suka fara
- Mutum 7 ’yan gida daya sun rasu bayan cin Dambu mai guba a Zamfara
A cewar Ministan, abin da ya sani shi ne kyautar motoci kirar Hilux da gwamnatin Zamfara ta ba wa kasarsa a mtasayin gudunmawa, su ma a bisa dalilin kawowa jama’ar jihar dauki kan ‘yan ta’adda ne.
Alkassoum ya ce gwamnatin Zamfara ta yaba da yadda sojojin Nijar din ke zuwa cikin gaggawa a duk lokacin da ’yan ta’adda suka kawo hari a kauyukan jihar da ke kan iyaka da kasar.
Su ma wadannan motoci guda biyar, jihar Maradi gwamnatin Zamfarar ta ba, kuma sun karbi guda hudu saura cikon daya, a cewar Ministan na Jamhuriyar Nijar.
Wani dan jarida, David Hundeyin, ne ya fara bankado labarin amincewar sayen motocin 10 kyauta ga jamhuriyar Nijar da shugaba Buhari ya yi, kafin daga baya Ministan Kudi Zainab Ahmed ta furta cewa an ware Naira viliyan 1.15 don sayen motocin
Ta kuma ce, tuni Shugaba Buhari ya sa hannu aka fitar da kudin domin sayo motocin, da kuma mika su ga kasar mai makwabtaka da Najeriya.