Motar daukar mai ta farko ta shiga Zirin Gaza tun bayan da Isra’ila ta hana shigar da mai yankin Falasdinawan kwanaki 38 da suka gabata.
A safiyar Laraba babbar motar da ke dauke da man ta shiga Zirin Gaza daga iyakar Rafah da ke kasar Masar.
Kafar yada labaran kasar Masar ta ce za a kai ma ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya “domin ci gaba gudanar da ayyukan jin kai a yankin Falasdinawan da ke fama da karanin mai”
Wasu ganau sun bayyana cewa karin wasu manyan motocin dakon mai guda biyu suna jiran tantancewa a iyakar Rafah domin su ma su shiga Gaza.
Rashin man fetur a Gaza ya tsayar da harkokin rayuwa da dama, inda asibitoci suka daina aiki, lamarin da ya yi ajalin kananan yara da sauran marasa lafiya asibitoci.
Mutanen da ke fama da raunuka da cututtuka masu hadari a Gaza sun shiga halin ha’ula’i kafin daga bisani a ba da izinin fitar da su zuwa wasu kasashe domin kula da lafiyar.
Gabanin fara yakin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, Falasdinawa sama da 20,000 ne ke zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsu, ciki har da masu fama da cututtuka irin su kansa da dangoginsu.
Yakin Isra’ila kuma ya yi sanadiyyar jikkata dubban mutane a Gaza, ga shi kuma rashin mai a asibitoci ya kaw cikas ga yadda jami’an lafiya ke duba mutane.