✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin dan kasuwa ya rataye kansa a Kano

Matashin dan kasuwar ya shiga damuwa bayan da wasu abokan kasuwancinsa suka damfare shi kayan da ya saya da kudaden rance

An tsinci gawar wani dan kasuwa mai mai shekaru 35 a duniya da ake zargin ya rataye kansa a wani daki da ke unguwar Sharada a Kano.

An gano gawar matashin dan kasuwar ce da wasikar da ya rubuta cewa: “A yi hakuri. Amma sauran ba sai na bayyana ba.”

Aminiya ta samu labarin cewa marigayin yana zaune ne a bangaren samari a gidan da lamarin ya faru shi da dan uwansa.

Dan uwan nassa mai suna Hamisu ya shaida mana cewa, “Na dawo daga sallar asuba, matata na shirin dafa wa ’ya’yanmu abinci, tana neman ashana domin ta kunna wuta amma babu.

“Sai ta tuna yakan yi amfani da ashana wajen kunna turaren wuta.

“Da ta aiki yaronmu ya karbo ashana a wajensa, sai yaron ya gan shi a rataye, sai ya koma da gudu yana ihu wai wani ne ya rataye yaya. Sai na garzaya daki na ga gaskiya ne”.

Da aka tambaye shi ko yana da wata matsala da marigayin, sai ya ce, “Ba mu samu wata matsala ba. Abin da na sani shi ne a kwanakin nan yana cikin damuwa, kuma a matsayinmu na ’yan kasuwa, mukan ji haka idan kasuwa ta yi sabanin yadda muke so.

“Mu ’yan kasuwa ne kuma muna sana’ar sayar da kayan daki, amma shi wani lokaci yana saye da sayar da tsofaffin kayan.

“Na lura da alamun damuwa a tare da shi a kwanakin nan saboda ya karbi kudi a hannun wani ya sayo kayan da kudinsu ya kai N400,000 a Rijiyar Zaki daga hannun wasu mutane suka kai shi gidan da suka ajiye kayan suka ce ya dawo wata rana ya kai su.

“Da ya nemi lambar wayarsu, sai suka ce tun da ya ga gidan zai iya dawowa kowane lokaci, amma da ya koma bai samu gidan ba.

“Abin da ya jawo masa damuwa ke nan domin kudin ba nasa ba ne kuma mai kudin ya matsa masa a kan ya biya shi,” in ji dan uwan nasa.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani bayani kan lamarin daga rundunar ’yan sandan jihar kan faruwar lamarin.