✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya Za Ta Binciki Soke Bizar ’Yan Kasarta 264 Da Saudiyya Ta Yi

Najeriya za ta binciki soke bizar ’yan kasarta 264 da hukumomin Saudiyya suka yi, bayan sun isa can domin Umrah da sauran harkoki

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta binciki soke bizar ’yan Najeriya 264 da hukumomin Saudiyya suka yi, bayan sun isa Saudiyya domin ibadar Umrah da sauran harkoki.

Fasinjojin dai sun tashi ne daga jihar Kano, da Kuma Jihar Legas a jirgin Air Peace, inda bayan saukar su a Saudiyya a sanar da soke bizar dukkansu.

Bayan da Saudiyya ta soke bizar su, ta kuma bukaci da jirgin ya dawo da su Najeriya.

Amma daga bisani ofishin jakadancin Najeriya ya sa ba ki, aka bar 87 daga cikinsu suka shiga kasar, yayin da aka dawo da 177 zuwa gida Najeriya.

A sanarwar da mataimakin ministan harkokin kasashen waje, kan kafofin watsa labarin, Alkasim Abdulkadir, ya fitar, ya ce ma’aikatar za ta bibiyi batun, domin samun cikakken bayanin abin da ya sa hukumomin Saudiyya daukar matakin.

Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance daga Saudiyya game soke bizar ’yan Najeriya da ta yi a ranar Lahadi. 

Saudiyya ta soke bizar ’yan Najeriyar ne duk da cewa Shugaba Tinubu na Najeriya yana kasar inda yake halartar taro tattalin arziki da nufin kulla alakar habaka cinikayya da zuba jari da sauran harkoki tsakanin kasashe biyu da ma sauran kasashen Larabawa.

A yayin ziyarar ta Tinubu ya yi zawarcin ’yan kasuwar Saudiyya su zuba jari a Najeriy, inda kasar Larabawan ta jaddada shirinta na taimaka wa Najeriya wajen gyara matatun manta da kuma samuwar kudaden kasashen waje.