A wani rahoto mai ban tausayi da ya faru a yankin French Quarter na birnin New Orleans a ƙasar Amurka, yayin da mota ta kutsa cikin wani cunkoson jama’a, inda mutane 10 suka mutu, wasu 30 suka jikkata.
Harin dai ya faru ne a titin Bourbon, wani shahararren wurin yawon buɗe ido, lokacin da motar ta bi ta cikin jama’a, a ranar Laraba da yamma.
- An raunata wasu a rikicin matasa da ’yan banga a Neja
- Tinubu ya shafe kwanaki 180 daga cikin 580 da ya yi na mulkinsa a ƙasar waje – Obi
Shaidu sun shaida wa kafar rediyo da talabijin ta CBS News cewa, direban ya fito daga motar ya fara harbin masu tafiya a kan hanya yayin da ‘yan sandan suka buɗe masa wuta, lamarin da ya yi sanadin jikkata wasu jami’ai biyu a yayin musayar wuta.
Sufeto ‘yan sandan New Orleans, Anne Kirkpatrick, ta bayyana harin a matsayin “babban ganganci.”
“Wannan mutumin yana ƙoƙari ya bi ta kan mutane da yawa kamar yadda ya yi yunƙurin yi,” in ji ta.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:15 na rana.
Kirkpatrick ta lura da cewa galibin waɗanda abin ya shafa da alama mazauna yankin ne, kodayake har yanzu ba a tabbatar da sunayensu ba.
Adadin waɗanda suka mutu da jikkata na iya canzawa yayin da ake ci gaba da bincike.
Hukumar FBI ta ɗauki nauyin binciken. A cewar wata jami’ar FBI, Althea Duncan, ba a bayyana harbin a matsayin harin ta’addanci ba, amma an gano wasu bama-bamai a wurin.
Hukumomi suna bincikar na’urorin don tantance ko za su iya aiki. Duncan ta buƙaci jama’a da su ƙauracewa yankin har sai an fitar sanarwa.
Gwamnan Louisiana Jeff Landry ya bayyana damuwarsa kan lamarin, yana mai bayyana harin a matsayin “mummunan tashin hankali.” Ya jajantawa waɗanda abin ya shafa tare da yaba wa jami’an da suka kai ɗauki a wurin.