✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mota ta kade dan tseren Kenya a Kolombiya

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Kolombiya sun  ce wata mota ta buge dan tseren gudin gudun famfalaki dan kasar Kenya, Joseph Kiptum a lokacin…

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Kolombiya sun  ce wata mota ta buge dan tseren gudin gudun famfalaki dan kasar Kenya, Joseph Kiptum a lokacin da ake gasar tseren gudun famfalaki da ake wa lakabi da Medellin Marathon.

dan tseren mai kimanin shekara 30 ya gamu da tsautsayi ne lokacin da yake jagorantar ’yan tsere kimanin 100 a gasar gudun famfalaki da kasar Kolombiya ta shirya a karshen makon jiya.

Rahoton ya ce, dan tseren wanda yake gab da lashe gasar, bai ankara ba sai ya ji mota ta make shi al’amarin da ya sa ya fadi a sume kuma ya samu raunuka a sassan jikinsa. Sai dai bayan an garzaya da shi asibiti likitoci sun yi nasarar farfado da shi, kuma sun yi masa magani suka sallame shi ya koma gida.

Rahotanni sun ce  dan tseren ya farfado kuma yana samun sauki.

Al’amarin ya faru ne bayan da direban wata motar dakon kaya ya yi biris da umarnin da aka ba masu motoci na kada su kuskura su bi hanyar da ’yan tseren suke amfani da ita wajen yin gasar.  Direban na cikin tafiya bai yi aune ba sai ya buge dan tseren tare da ji wa wadansu da dama rauni.

Tuni jami’an tsaro a kasar suka shiga bincike bayan sun kama direban motar, don gano musabbabin faruwar al’amarin.