Mohammed Bazoum ya zama zababben Shugaban Jamhuriyar Nijar kuma Shugaban Kasa zababbe na farko da ya karbi mulki daga zababbiyar gwamnati ta hanyar dimokuradiyya a tarihin kasar.
Bazoum ya lashe zaben Shugaban Kasar da kashi 55.7%. Rikicin bayan zaben na ranar 21 ga Fabrairu ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da kuma tsare wasu 470. Daga baya kotu ta tabbatar da nasararsa.
An haifi sabon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum a shekarar 1960.
Shi Balarabe ne daga yankin Diffa, Jihar Damagaram ta kasar.
Ya yi karatunnsa na firamare har da sakandare ne a Zinder.
Bayan karantar ilmin Falsafa a jami’a a 1984, Bazoum ya zama malamin makaranta, inda ya koyar da ilimin falsafa a Maradi da kuma Tahuoa.
Ya kasance dan gwagwarmayar kwadago da siyasa inda tun daga kungiyar malamai ya shiga fafutikar kwato hakkin ma’aikata.
Yana cikin ’yan gwagwarmayar kwadagon da suka tabbatar da ganin gamayyar kungiyoyin kwadagon sun kafa jam’iyyar PNDS Tarayya da kuma zaben Shugaba Mahamadou Issoufou a 2011.
An nada Bazoum a matsayin minista sau hudu, sau biyu kuma ana zaben sa a matsayin dan majalisa.
A 1995 ya fara zama Ministan Harakokin Kasashen Waje a gwamnatin hadin gwiwar MNSD Nasara da PNDS Tarayya ta Hama Amadou, matsayin Firaminista a lokacin.
Ya sake rike mukamin a Gwamnatin soji ta Shugaba Ba’are Mainasara bayan ta kifar da gwamnatin hadin gwiwar a 1996. Daga baya ta sallame shi saboda adawa da ita.
Bazoum ya sake zama Ministan Harakokin Waje daga 2011 zuwa 2015.
Kafin nan shi Sakataren Harakokin Waje a Ma’aimakatar ce takanin 1991 da 1993 zamanin gwamnatin rikon kwarya ta Amadou Cheiffou.
Shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PNDS Tarayya a lokacin da Mahamadou Issoufou yake Shugaban Jam’iyyar.
Bayan zaman Issoufou Shugaban Kasa, sai Bazoum ya zama Shugaban Jam’iyyar a 2011.
A 2015 Gwamnatin Mahamadou Issoufou ta nada shi Minista a Fadar Shugaban Kasa.
Ya zama zababben dan majalisa karkashin jam’iyyar PNDS a 1993 amma daga baya aka soke zaben.
A 2016, an zaben shi a matsayin dan majalisa. Daga baya Shugaba Issoufou ya nada shi Ministan Harakokin Cikin Gida tsakanin 2016 zuwa 2021.
A 2021 ya yi murabus daga mukamin domin tsayawa takarar Shugaban Kasa na watan Fabrairu.
Ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben da kashi 57.7% kuma ana kallonsa a matsayin dan gaban goshin tsohon shugaban kasar.
Ya yi alkakawarin dorawa a kan ayyukan da Shugaba Issoufou ya fara na tabbatar da tsaro, farfado da tattalin arziki.
Kwana biyu kafin rantsar da Bazoum, wasu sojoji sun yi yunkurin juyin mulki, amma aka dakile harin da suka nemi kaiwa Fadar Shugaban Kasar aka kuma kame su.