✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Modric ya zama Gwarzon Dan Kwallon Duniya na 2018

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen dan kasar Kuroshiya, Luka Modric ya zama Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya na bana…

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen dan kasar Kuroshiya, Luka Modric ya zama Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya na bana a ranar Litinin da ta wuce bayan ya doke Cristiano Ronaldo na kulob din Jubentus da ke Italiya da Lionel Messi na kulob din FC Barcelona da ke Sifen.

Modric ya kasance dan kwallo na farko da ya taka wa Ronaldo da Messi birki bayan da suka rika lashe wannan kyauta a tsawon shekara goma a tsakaninsu, inda kawo yanzu kowannensu yake da biyar-biyar.

Rabon da wani dan kwallo ya lashe wannan kyauta in ba Ronaldo ko Messi ba, tun shekarar 2007 lokacin da dan kwallon AC Milan dan asalin Brazil Kaka ya lashe.  Tun daga wancan lokaci ne Ronaldo da Messi suka rika lashe ta sai a bana da Modric ya taka musu birki.

Modric ya samu nasarar lashe kyautar ce saboda yadda ya taimaki kulob din Real Madrid wajen lashe kofin Zakarun Kulon na Turai sau uku a jere sannan ya taimaki kasarsa Kuroshiya zuwa wasan karshe a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Rasha.

Sauran ’yan kwallon da suka fafata a gasar sun hada da Cristiano Ronaldo da ya zo na biyu sai Kylian Mbappe dan kwallon PSG da ya taimaka wa Faransa lashe Kofin Duniya ya zo na uku sai Antoine Griezmann dan kwallon Atletico Madrid da ke Sifen da shi ma ya taimaki Faransa lashe Kofin Duniya a Rasha ya zo na hudu yayin da Lionel Messi ya kasance na biyar.

Modric, dan shekara 33 wannan ne karon farko da ya taba lashe wannan kyauta.