Assalamu alaikum wa rahmatullah, barka da sake haduwarmu cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Na samu tambayoyin masu karatu daban-daban game da bayanin da ya gabata a kan matsalar matasan magidanta, (MMM), ga bayani da zai amsa dukkan tambayoyin da kuka aiko.
Robali
Masu karatu da yawa sun aiko da tambaya, suna son sanin ko mece ce robali; abin ya ba ni mamaki kwarai da gaske, domin na zaci robali dai sunanta robali a ko’ina a kasar Hausa; robali dai ita ce siririn dankon nan da ake amfani da shi wajen daure kudi a bankuna. Hakan nan wasu sun tambaya a daidai ina ne ya kamata a sanya robalin? To za a sa a wajen da aka yi kaciya ne, kuma ba a son ya wuce tsawon minti 30, da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Tsaidau
Makaranta da yawa sun aiko tambayoyinsu suna neman karin bayani kan tsaidau da kuma yadda ake amfani da shi.
Tsaidau dai wani tsiro ne mai bin kasa yana yado, yana da wasu mulmulallun kayoyi masu tsinin daga uku zuwa biyar. Wannan kayar ce tasa ake ce masa tsaidau, domin indai ka bi ta wajen da yake, komai dabararka sai ka taka kayar, wacce za ta sa ka tsaya cirewa. Haka kuma shi ya sa ake ce masa hana takama, domin ba yadda za a yi tafiya cikin takama a inda ya kasance akwai tsaidau a shuke, dole sai dai a taka sannu-sannu gudun kada a taka kayarsa. Da fullanci ana kiransa da sunan tsaiji; da kanuri kuma kaije; da yaren shuwa-arab kuma daraisa; da turanci ana kiranta da puncture bine.
Yadda za a Sarrafa Tsaidau: Gaba daya tsiron za a tugo daga kasa hade da saiwarsa, sai a wanke a raba shi da duk kasar da like a jikinsa, sannan sai a shanya ya bushe, sai a dake shi a tankade, a rika shan karamin cokali daya cikin ruwa, nono, ko a barbada a saman abinci, sau daya a rana kullum, har sai an ga bayan matsalar. Mu tuna, ba a hada shan shi tare da wani magani kowane iri ne, kuma musamman ma magungunan hawan jini, ciwon zuciya da na ciwon suga; kuma a sha shi sannu-sannu, kar a wuce karamin cokali daya a rana. Sannan ba wai a sha maganin ba ne kadai, sai an hada da sauran hanyoyin da bayanin su ya gabata, musamman na kwarewa wajen iya jan ragamar sha’awa; da fatan Allah Ya kawo waraka ga dukkanin masu fama da wannan matsala, amin.
Tambaya: “Ba ni da aure, kuma na kasance a da ina yawan yin zinar hannu, to sai na bi hanyoyin da kika ambata don kaucewa kamuwa da matsalar MMM, ko kuwa tun da na bari shi ke nan?”
Musa daga Katsina
Amsa: Ba laifi kana iya yi kamar yadda na yi bayani na tsawon wata uku zuwa shida don inganta jijiyoyin al’aura daga raunin da yin zinar hannu ke haifar masu. Bayan nan kana da zabin ka ci gaba da yi ko ka bar shi haka nan, domin dai kegel ba shi da wata illa ga lafiyar jiki.
Tambaya: “Kin yi magana kan karfafa jijiyoyin al’aura ta hanyar kegel, to hakan ba zai haifar da matsala ga mara ko koda ba? Don in na yi na kan ji zafi kamar fitsarin zai koma cikin marata!”
Abu Ammar Kano
Amsa: Kegel bai haifar da wata matsala ga mara ko koda, sai dai ya gyara da ingantasu, domin asali, da ma don inganta mafitsara aka samar da shi, gam-da-katar ne aka yi da kasancewa har jijiyoyin al’aura ma yana gyarawa. Zafin da kake ji na rashin sabo ne, da ka saba, ka kware za ka daina ji cikin yardar Allah SWT. Wata kila kuma kana rike fitsarin ne fiye da sakan biyar, wannan dole kuwa ka ji zafi saboda rashin sabo. Ka fara da rike shi na tsawon sakan uku zuwa biyar, sai ka kware sakan biyar din ne sannan ka kara zuwa sakan goma zuwa sha biyar, da haka har ka shiga mintuna. Da fatan Allah Ya taimaka, ya ba da ikon dagewa, amin.
Tambaya: Idan mutum ya daina zinar hannu ana sauran wata 4 daurin aurensa; ko zai kubuta daga matsalar fitar maniyyi da wuri?
Wani Bawan Allah
Amsa: Ba a iya ganewa, amma dai an ce rigakafi ya fi magani, don haka sai a tari matsalar tun kafin ta faru ta hanyar bin dukkan hanyoyin samun warkewarta.
Sai sati na gaba in Allah Ya kai mu, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.
MMM: Amsoshin tambayoyinku
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barka da sake haduwarmu cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa,…