Ministan Gona Dokta Akinwumi Adesina ya kaddamar da sabon tsarin tallafa wa manoma a Jihar Zamfara a ranar Talata
Tsarin ya kunshi yi wa manoma aiki kyauta a gonakinsu ta hanyar amfani da motocin noma na mallakar gwamnatin tarayya.
Ministan ya ce bayan samar wa manoma takin zamani wanda ake cire musu kashi 50 cikin 100, yanzu Gwamnatin Tarayya ta fito da wannan sabon tsari ne don ta samar wa manoma hanyar da za su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin sauki, aka kuma rika musu noma kyauta.
Ya ce wannan tsarin zai taimaka wa manoma samun saukin biyan basussukan da suka karba, inda a bana gwamnati za ta yi wa manoma aiki wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 193 a kyauta.
Ya ce kayayyakin da gwamnati ta raba kyauta a wannan shekara kudinsu ya kai Naira biliyan 144 kyauta, inda a wannan shekarar manoma 594 ne suka amfana, musamman kan abin da ya shafi taki da irin shinkafa da kuma magunguna da dai sauransu.
Ya ce “Gwamnati ta ga dacewar ta fara kaddamar da wannan shiri a Jihar Zamfara saboda yadda jihar ta zo ta farko wajen biyan bashin da aka ba manoman jihar a shekarun baya, wanda aka cire masu kashi 25 cikin 100, gwamnatin tarayya ta gamsu da kwazon da manoman jihar nan.”
Kamar yadda aka bayyana za a ajiye wadannan motocin ne a kananan hukumomi daban-daban don abin ya zama da sauki ga kowane manomi idan ya tashi neman a yi masa aiki a gonarsa, “an yi hakan ne don a inganta aikin noma da kuma samar da aikin yi a kasar nan.”
Alhaji Shu’aibu Abdulsalam Magami shi ne Shugaban kungiyar Manoma na Gaskiya na Jihar Zamfara ya bayyana farin cikinsu sakamakon fara wannan tsari a jiharsu, musamman ma ganin yadda jiharsu ta zama ta farko wajen biyan bashi.
Ya ce “A Jihar Zamfara manoma sun samu saukin rage kashi 50 cikin 100 na duk abin da aka bayar, muna godiya, sannan ka isar da sakon godiyarmu ga shugaban kasa.”
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, ya mika godiyasa ta musamman ganin yadda a lokacinsa ne manoman Jihar Zamfara suka fara amfana da wannan tsari na kason kashi 50 cikin 100.
“Ina fata al’ummar Jihar Zamfara za su saka wa shugaban kasa da alheri, musamman idan lokacin yi hakan ya zo.” Inji Gwamnan.