Ministan Ayyuka da Sufuri na kasar Uganda, Janar Katumba Wamal ya tsallake rijiya da baya sakamakon yunkurin kashe shi da aka yi ranar Talata.
Kamfanin Dillancin Labarai na NBS ya ruwaito cewa duk da yake maharan ba su sami nasarar kashe ministan ba, amma sun kashe ’yarsa.
- Buhari na neman majalisa ta amince da sabon shugaban Sojin Kasa
- A gaggauta ceto daliban Islamiyyar Tegina —Buhari
A cewar rahotanni, maharan sun harbi motar ministan ne a wani kauye da ke wajen babban birnin kasar na Kampala.
Kazalika, an kuma kashe direba da kuma ’yar ministan, yayin da shi kuma aka garzaya da shi zuwa asibitin Medipal inda yanzu haka yake can yana samun kulawa.
Janar Katumba dai ya taba zama shugaban sojojin kasar da kuma na ’yan sanda kafin daga bisani a nada shi mukamin na Ministan Ayyuka da Sufuri a watan Disambar 2019.