Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar Portugal, Eduardo Cabrita, ya yi sauka daga mukaminsa bayan motarsa ta kade wani mai sharar titi.
Cabrita, wanda tsohon Mataimaikin Fira Ministan kasar ne, ya yi murabus din ne bayan motar gwamnatin da dauko shi a ciki ta kade wani ma’aikaci da ke sharan hanya har lahira.
“Na mika takardar sauka daga mukamina na gwamnati, ba na so a yi amfani da abin da ya faru a matsayin makamin siyasa,” a yaki gwamnati inji shi.
Tuni dai Fira Minista Antonio Costa, ya “amince da saukarsa daga mukamin nasa,” kamar yadda Mista Costa ya shaida wa wani taron ’yan jarida.
Murabus din ministan na zuwa ne kasa da wata biyu kafin zaben ’yan majalisar dokokin kasar Portugal da za a gudanar bayan majalisar ta yi watsi da kasafin 2022 da gwamnatin Mista Costa mara rinjaye a majalisar ta gabatar.
A watan Yuni ne motar gwamnati da ake tuka Mista Cabrita a ciki ta kade wani ma’aikaci da ke tsaka da sharan titi ta kashe shi yakin Evora da ke Kudancin kasar.
A ranar Juma’a an yi ta zargin direban ministan da aikata kisa da kuma sakaci da aikinsa.
Tun bayan hatsarin dai ake ta sukar gwamnatin da yi wa batun rikon sakainar kashi, gami da zargin minsitan da sakaci da aiki da kuma rashin tausaya wa iyalan mamacin.
Washegarin hatsarin, Cabrita ya ce a lokacin da abun ya faru, masu gyaran hanya ba su sanya wata alama da ke nuna ma’aikata na aiki ba a lokacin.
Amma bayan kwanaki kadan kamfanin da ke aikin ya musanta zargin, da cewa an sanya “cikakkun alamun nuna ana gudanar da aikin gyaran hanya.”
A 2017 ne dai aka nada Mista Cabrita a matsayin minista bayan tashin wata gobarar daji da ta yi ajalin sama da mutum 100 a kasar Portugal.