Mahmud Hassan, daya daga cikin wadanda aka kama da zargin shigo da bindigogi guda 661 a Disambar bara ya shaida wa Babban Kotun Abuja cewa Naira miliyan 1 ya biya jami’an tsaro sirri na DSS da sauran jami’an tsaro kafin ya fitar da kwantenarsa daga tashar jirgin ruwan Apapa.
Mahmud Hassan wanda tsohon mataimakin kwanturola ne na Kwastam, ya bayyaba hakan ne a lokacin da yake bayar da amsoshi a game da yadda ya shigo da makaman a wani faifan bidiyo da aka dauka tun watan Maris na bara wanda wani jami’in DSS ya gabatar a gaban kotu jiya.
“Na biya Naira miliyan 1 domin in fitar da kwantenata daga tashar jirgin ruwa ta Apapa, amma ba wai na biya kudin bane saboda makaman.,” in ji shi
Hassan ya kara da cewa da farko amince zai shigo da kwantenar a kan kudi Naira miliyan 3.8 a lokacin da aka ce masa kayan da ke ciki kofofi ne, amma daga baya da ya san cewa akwai bindigogi guda 661, sai ya kara kudin da za a biya shi zuwa Naira miliyan hudu.