✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Milgoma: Tsohon Shugaban PDP na Sakkwato ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Milgoma.

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Milgoma, rasuwa.

Ibrahim Milgoma ya rasu ne a daren Talata a Asibitin Zenith da ke Abuja.

Margayin sanannen dan siyasa ne da ke da akida da ya yi gwagwarmaya don tabbatar da gaskiya a mulki.

Ibrahim Milgoma ya taba rike shugabancin jam’iyyar shekara hudu a matakin jiha.

Dan kasuwa ne da yake taimakon jama’a a lokacin rayuwarsa, kuma ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya da jikoki.

Alhaji Yusuf Dingyadi ne ya sanar da rasuwar a kafarsa ta Facebook.