✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Miji ya saki matarsa kan yin ‘chatting’ da makwabcinsa

Wani magidanci ya bukaci kotu ta raba aurensa da matarsa bisa zargin ta da cin amanar aure da yin hira da makwabcinsa ta shafukan zumunta.

Wani magidanci ya bukaci kotu ta raba aurensa da matarsa bisa zargin ta da cin amanar aure da yin hira da makwabcinsa ta shafukan zumunta.

Da yake jawabi a gaban kotun, magidancin ya zargi matarsa cewa sau uku tana tafiya ta bar gidansa, ciki har da wani lokaci da ta bar gidan nasa na tsawon wata biyu.

Ya kuma zarge ta da alaka da wani makwabcinsa wanda take daukar tsawon lokaci tana hira da shi ta intanet.

Ya ce, “Lokacin karshe da ta bar gidan sai da ta dade kafin ta dawo, da ta dawo kuma sai ta kwashe kayanta.

“Na gaji da yadda take wulakanta zaman aure, saboda haka ina bukatar kwanciyar hankali,” in ji shi.

Amma a martaninsta, matar ta bayyana wa kotun cewa mijin nata, “Ba shi da hakuri, yana zargi na da cin amanar aure ba bisa hakki ba, har ya taba sawa an tsare ni a sel din ’yan sanda.

“Na yarda a raba auren, na gaji da yadda yake duka na, zargin cin amanar auren ya ishe ni haka.”

Daga karshe kotun da ke zamanta a Ighando a Jihar Legas ta raba auren saboda abin dta kaira cin amana, sakaci da aure da kuma rashin zama tare.

Shugaban kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce raba auren shi ne zai kawo karshen takaddamar, sannan ya umarci mijin da ya biya matar Naira dubu 250.