Wani dan kasuwa, mai suna Nura Ashiru, ya bukaci matarsa Zainab Bello wadda ta nemi da ya sake ta da ta biya shi Naira miliyan 1.5 a wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, a Jihar Kaduna.
Ashiru ya gabatar da bukatarsa ne bayan da matarsa ta bukaci kotu ta datse igiyar aurensu ta hanyar Khul’i, wato hanyar da mace ke mayar da sadakin da ta karba domin ta fanshi kanta daga auren.
- Messi ya sake lashe kambun Ballon d’or a karo na 8
- Shin ya kamata a goyi bayan mulkin shekara shida-shida a Najeriya?
“Matata ta yi min babbar asara. Ta lalata wayata ta kwashe wasu kayana, lamarin da ya sanya ni cikin bacin rai,” in ji shi.
Ya kuma roki kotun da kada ta bai wa matarsa rikon dansu ko da ta raba auren.
Tun da farko dai mai shigar da kara ta shaida wa kotun cewa a shirye ta ke ta mayar da kudin sadakin Naira 80,000 da ta karba daga hannun wanda ta ke kara sannan ta roki da kotun ta ba damar rikon yaronsu dan shekara uku a duniya.
Sai dai wadda ta shigar da karar ta musanta lalata wayar mijinta.
Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahma, ya dage sauraren karar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba domin wanda ake kara ya gabatar da shaidunsa.