A bana Emmanuel Gyang da matarsa Deborah Pam Badung sun zamo zakarun gasar tsere ta maza da mata ta Yaki da Cin Hanci da Rashawa kashi na biyu da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata a Birnin Tarayya, Abuja.
Gasar tseren ta kilomita 21.03 wacce aka fara ta daga Dandalin a Eagle Skuare an shirya ta ce don karfafa Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta bana.
Gyang wanda ya zo na uku a bara, ya zama zakara bayan da ya kammala tseren a cikin awa 1 da minti 6, wanda hakan ya sanya ya samu kyautar Naira miliyan daya.
Kamar yadda ya fada, ya shirya wa gasar sosai a bana bayan ya kasance na uku a bara.
“A bana na yi shiri na musamman, na ba wa kaina horo sosai don ganin na cimma burina. Na zo na uku bara amma bana ni ne na zo na daya,” inji shi.
A nata bangare Deborah ta ce ba ta yi wani kyakkyawan shiri ba amma dai ta ci sa’a ta samu nasarar zama ta daya bayan da ta kammala tseren a cikin awa 1 da minti 9. Daga nan ta bukaci a ci gaba da ba su goyon baya don kaiwa ga wani mataki.
“Ya dace a ce an kai mu wata kasa mun yi sansani don ganin yadda suke aiwatar da irin wannan gasa tasu. Kuma ka ga a nan ba mu da ma’aikatan lafiya da za su kula da lafiyarmu idan mun ji ciwo,” inji ta.
Da yake magana a karshen gasar, Shugaban Shirya Gasar, Mista Jocob Onu, cewa ya yi manufar gasar ita ce a isar da sakon wayar da kan al’umma a kan muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa.
“Tun a farkon gasar mun bayyana manufarmu karara cewa makasudin wannan gasa ita ce, a ilimantar da jama’a a kan illar cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma. A wannan karon mun kara wa abin armashi ta hanyar kaddamar da tarurruka a wasu jami’o’i,” inji shi.