✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya zama Gwarzon Dan Kwallon Duniya karo na 6

A ranar Litinin da ta wuce ce wata mujalla da ake wallafawa a Faransa  da ke shirya Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya kowace shekara da…

A ranar Litinin da ta wuce ce wata mujalla da ake wallafawa a Faransa  da ke shirya Gasar Gwarzon Dan Kwallon Duniya kowace shekara da aka fi sani da Ballon D’or ta bayyana Lionel Messi dan asalin Ajantina kuma dan kwallon FC Barcelona na Spain a matsayin wanda ya lashe gasar ta bana.  Wannan shi ne karo na 6 da Messi yake lashe kambin kuma ya shiga kundin tarihi.

Messi ya samu wannan nasara ce a bikin karrama ’yan kwallo da aka yi a Paris babban birnin Faransa.

Birgil Ban Dijk dan kwallon Liberpool da ke Ingila ne ya zama na biyu yayin da Cristiano Ronaldo dan kwallon Jubentus da ke Italiya ya zama na uku sai Sadio Mane dan kwallon Liberpool na Ingila ya kasance na hudu.

Ronaldo ne yake biye da Messi bayan ya lashe gasar sau biyar.

Sai dai wadansu da dama sun bayyana rashin gamsuwa game da yadda aka zabi Messi a bana, kasancewa in ban da kofin La-Liga na Spain bai lashe wani kofi a bara ba.

An zabi Messi ne saboda ya fi yawan zura kwallaye a raga a Nahiyar Turai a bara.