✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya tsallake zuwa jarun da ya biya harajin Naira biliyan daya

A ranar Talatar da ta wuce ne kafofin watsa labarai suka sanar da cewa shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi ya…

Lionel MessiA ranar Talatar da ta wuce ne kafofin watsa labarai suka sanar da cewa shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Lionel Messi ya tsallake tafiya gidan kaso bayan ya biya bashin harajin da ake binsa na Fam miliyan 4 da dubu 200 kwakwantacin Naira biliyan daya.
Rahotanni sun nuna mahukunta kasar Sifen sun maka dan kwallon a kotu ne tun a watan Yunin da ya gabata inda ake tuhumarsa da laifin kin biyan haraji na wadansu shekaru.
Rahoton ya kara da cewa a ranar 17 ga watan Satumbar da muke ciki ne ake sa ran cigaba da sauraron karar amma tun da dan kwallon tare da mahaifinsa sun bayar da kai bori ya hau ma’ana sun biya dukkan basussukan da ake binsu, yanzu maganar cigaba da sauraron karar ta sha ruwa kenan.
Rahoton ya ce da Messi ya kuskura an tabbatar da laifinsa na kin biyan haraji a kotu da ya shafe kimanin shekara  shida a gidan kaso.
Tuni Lauyan da ke kare Messi da mahaifinsa ya gabatar da bukatar a daina cigaba da sauraron karar tun da abokin huldarsa ya cika ka’idar da ake nema na biyan harajin ba tare da ya bata lokaci ba.