Ɗan wasan gaba na Argentina, Lionel Messi ya sanya hannu kan kwantaragi da ƙungiyar Inter Miami da ke Amurka wadda za ta kai har shekarar 2025.
Messi, wanda ya lashe kyautar ɗan wasan duniya ta Ballon d’Or har sau bakwai, ya bar ƙungiyar PSG ta Faransa ne a ƙarshen kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
- Kofin Duniya 2026: Yadda kasashen Afirka za su fafata wajen neman tikiti
- Mai ’ya’ya 8 ta sake haifar ’yan 3 a Kebbi
Messi, wanda ya jagoranci tawagar ƙasarsa wajen lashe kofin duniya a Qatar a bara, ya ce: “Ina matuƙar farin cikin buɗe wani sabon babi a sana’ata a Inter Miami kuma a Amurka.”
Ɗaya daga cikin mamallakan ƙungiyar ta Inter Miami, David Beckham ya ce sayen Messi da ƙungiyar ta yi “abu ne tamkar a mafarki.”
Messi, wanda a baya bai taɓa buga wa wata ƙungiya wasa ba a wata nahiyar baya ga Turai, ya ƙara da cewa: “Wannan babbar dama ce kuma za mu yi aiki tare wajen cimma nasara.”
Inter Miami ƙungiya ce da ke wasa a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka, wato MLS, kuma da yiwuwar zai buga wa ƙungiyar wasa a karawar da za ta yi da Cruz Azul ta ƙasar Mexico a ranar 21 ga watan Yuli.
Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai kuma ana sa ran zai iya sake lashe kyautar a bana, bayan jagorantar ƙasarsa wajen lashe Kofin Duniya.
Ɗan wasan ya ci wa PSG ƙwallaye 32 a wasa 75 da ya buga mata. A kakar da ta gabata ya ci kwallo 16, ya taimaka an ci wasu 16 a gasar Lig 1 ta Faransa.
Messi ya koma PSG ne a shekarar 2021 bayan ya kwashe shekara 21 a Barcelona.
Kuma shi ne ya fi kowane ɗan ƙwallo ci wa Barcelona ƙwallaye a tarihi, inda ya zura ƙwallo 672, ya lashe gasar La Liga 10, da gasar zakarun Turai ta Champions League huɗu, da kuma Spanish Cup bakwai.