✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai ’ya’ya 8 ta sake haifar ’yan 3 a Kebbi

Sai dai ta rika zubar da jini bayan haihuwar

Wata mata mai ’ya’ya takwas a garin Zauro da ke kusa da Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, ta haifi ’yan uku, duka maza.

Matar mai suna Fadimatu Aliyu Labbo, ta haihu ne ranar Juma’a.

A cewar shugabar sashen kula da haihuwa asibitin kwararru na Yahaya, Felicia Paul, matar ta zubar da jini sosai lokacin da aka kai ta asibitin bayan ta haihuwa a gida. Daga bisani an garzaya da ita asibitin.

Ta bukaci mata da su daure su rika zuwa asibiti domin haihuwa saboda yin hakan a gida ba tare da kwararrun ma’aikatan lafiya ba yana da hatsari sosai.

A wani labarin kuma, matar Gwamnan Jihar ta Kebbi, Hajiya Zainab Nasare, ta bayar da tallafin kayan abinci da kudi ga iyalan matar.

Da take gabatar da kayan, mai ba Gwamnan Jihar shawara a kan harkokin mata, Hajiya Udu Sani, ta ce tallafin wani tagomashi ne na matar Gwamnan a kokarinta na magance matsalolin mata a Jihar.

Da yake tsokaci a kan tallafin, miji matar, Malam Aliyu Labbo Zauro, ya ce ya ji dadi sosai da tallafin matar Gwamnan da ma haihuwar ’yan ukun.