✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta sake bude iyakar Kamba a Kebbi

Hukumar ta jaddada haramcin fita da kayan abinci zuwa kasashen ketare.

Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Kasa a Jihar Kebbi, Iheanacho Ojike, ya sake bude iyakar Kamba bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na bude iyakokin Jamhuriyar Nijar nan take.

Kakakin hukumar, Mohammed Tajuddeen Salisu ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Jim kadan bayan bude kan iyakar, Hakimin Kamba, Alhaji Mamuda Fana, masu ruwa da tsaki da sauran hukumomi sun halarci sake bude iyakar, inda ya bayyana ta a matsayin iyaka mai samar da kudaden shiga a Kebbi.

Ya kara da cewa, an bude iyakokin ne da nufin dawo da harkokin kasuwanci da za su yi tasiri wajen gina kasa, da kuma hana shigo da haramtattun kayayyaki.

Ojike ya jaddada cewa jami’an rundunar sun shirya saukaka harkokin kasuwanci tare da yin aiki da doka a iyakar Kamba matukar za a shigo kayayyaki ta hanyar bin dokokin kwastam da biyan kudade zuwa asusun gwamnatin tarayya.

Kazalika, ya jaddada cewar gwamnati ba ta ɗage haramcin fitar da hatsi ko kayan abinci zuwa kasashen waje, duba da yadda ake fama da karancin abinci a fadin kasar nan.

Hakimin Kamba, Malam Fana, ya yaba wa kokarin gwamnatin tarayya, ya kuma jaddada cewa wannan wani mataki ne da al’ummar yankin za su inganta sana’o’insu.