✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Dahiru Mangal ta rasu

Kawo yanzu babu wani bayani dangane da batun shirye-shiryen jana’izarta.

Allah Ya yi wa matar hamshakin attajirin nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal rasuwa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Hajiya Aisha Mangal ta rasu ne da Yammacin wannan Asabar.

Bayanai sun ce ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja inda ta yi ’yar gajeruwar rashin lafiya.

Sai dai ya zuwa hada wannan rahoto babu wani bayani dangane da shirye-shiryen jana’izarta.