Hamshakin dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Barau Managal, na ci gaba da karbar manyan mutane a ziyarar ta’aziyyar rasuwar matarsa.
A ranar Laraba ce tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bi sahun mutane wajen ta’aziyyar marigayiya Hajiya A’isha Dahiru Mangal da ta rasu.
- Majalisa za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama
- Tsadar Fetur: COEASU ta umarci malamai su koma aiki sau 2 a mako
Ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja a ranar Asabar, bayan ta sha fama da rashin lafiya kuma an yi jana’izar ta a Katsina a ranar Lahadi.
Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya yi wa Buhari rakiya zuwa gidan na Mangal.
Mataimaki na musamman ga tsohon Shugaban, Sabi’u Yusuf Tunde, na tare da Buhari yayin ziyarar.
Tsohon Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayiyar ya kuma bai wa iyalan Mangal hakurin jure rashin da suka yi.
Yayin da yake Katsina, Buhari, tare da rakiyar Gwamna Radda,ya kuma kai ziyarar ban girma da ta’aziyya ga Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, a fadarsa.
Kazalika, tsohon Shugaban ya halarci taron ci gaban gidauniyar Katsina na 2023 wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Katsina.
Sauran manyan mutanen da suka je Katsina domin ta’aziyyar sun hada da Gwamnonin Kano da Zamfara, Abba Kabir Yusuf da Dauda Lawal.
Haka kuma jagoran Kwankwasiyya na kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin wadanda suka kai ziyarar ta’aziyyar.