✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama

Majalisar ta bukaci kwamitin da za ta kafa ya kammala bincikensa cikin lokaci

Majalisar Wakilai ta kuduri aniyar bai wa kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama dama ya binciki yadda gwamnatin da ta shude ta cefanar da wasu filayen jiragen sama.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Kama Nkemkanma ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce, an jinginar da filayen saukar jiragen sama masu muhimmanci ga kamfanonin kasashen waje ta hanyar kudirin majalisar zartarwa ta tarayya, wanda da ya ce sun kauce wa bin ka’ida.

A cewarsa, a karshe sakamakon ba da jinginar da filayen jiragen wasu tsirarun ‘yan Najeriya marasa kishin kasa ya azurta.

Ya ce, “Manyan filayen jiragen samanmu na Legas, Abuja, da Kano kullum ana tafka cece-kuce saboda muradin kashin kai da suka yi wa dokokin kasa zagon kasa, ba tare da la’akari da kokarin da hukumominmu na yaki da cin hanci da rashawa ke yi a wasu lokuta ba.”

Nkemkanma, ya ce a halin yanzu ‘yan Najeriya na fuskantar asarar ayyukan yi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin al’ummar da za su zo nan gaba saboda manufar jinginar da filayen jiragen saman.

Don haka majalisar ta yanke shawarar cewa kwamitin wucin gadin ya binciki jinginar da filayen jiragen saman Najeriya sannan ya bayar da rahoto cikin mako uku don daukar mataki na gaba.

A karkashin shugaban tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika aka jinginar da filayen jiragen saman.

Sai dai hakan ya tada kura a zauren majalisar.