✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar Fetur: COEASU ta umarci malamai su koma aiki sau 2 a mako

Kungiyar Malaman Kwalejin Ilimi ta Kasa (COEASU) ta bai wa mambobinta umarnin takaita zuwa aiki zuwa sau biyu a sati. Kungiyar ta ce umarnin zai…

Kungiyar Malaman Kwalejin Ilimi ta Kasa (COEASU) ta bai wa mambobinta umarnin takaita zuwa aiki zuwa sau biyu a sati.

Kungiyar ta ce umarnin zai fara aiki ne nan take har zuwa lokacin da za ta gudanar da taron gaggawa domin yanke adadin kwanakin da ya kamata malaman su cigaba da zuwa aiki.

Shugaban Kungiyar Dokta Smart Olugbeko ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce duk da cewa karin kudin man fetur da gidajen mai suka yi a safiyar ranar Talata zai jefa ma’aikatan cikin kunci, za su ci gaba da jurewa, domin suna da kwarin guiwar gwamnatin tarayya za ta samar musu da mafita.

“Cire tallafin man fetur da gwamnatin taryya ta yi watanni biyu da suka gabata ya sa an samu karin farashin man fetur da kashi 250, wanda hakan kuma ya haifara da hauhawar farashin masarufi, sufuri da sauran bangarorin rayuwar talaka.

“Sai dai muna da yakinin gwamnatin za ta samar wa ‘yan Najeriya musmaman ma’aikatanmu mafita ta hanyar raba tallafi da kara mana albashi” in ji shi.