✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amarya ta sha da kyar a hannun ’yan bindiga lokacin da ake kokarin kai ta gidan miji

Dole amaryar ta cire kayan bikin, ta ranta a na kare cikin daji

Wata amarya a Jihar Neja ta cire rigar bikinta sannan ta ranta a na kare tsawon kilomitoci a cikin daji don guje wa harin ’yan bindiga.

Rahotanni sun nuna maharan sun farmaki amaryar ne lokacin da ake shirin kai ta gidan mijinta.

Aminiya ta gano cewa an dauki amaryar ce daga wani kauye a Karamar Hukumar Paikoro, inda za a kai ta Kuta, hedkwatar Karamar Hukumar Shiroro, amma maharan suka tare tawagarta a daidai garin Kaffin-Koro da ke Karamar Hukumar Paikoro ta Jihar.

Wata ’yar uwar amaryar da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, “Mun dauki amaryar ne daga kauyenmu za mu kai ta Kuta. Muna kan hanya ne sai ’yan bindiga suka kai mana hari a daidai garin Kaffin-Koro.

“Amaryar na sanye da rigar bikinta a daya daga cikin motocin da ke baya a lokacin, nan take sai ta cire ta. A nan ne ’yan bindigar suka tarwatsa mu zuwa cikin daji.

“Sun sace kawayen amarya su biyu, amma su ma daga bisani sun tsere, dole aka dage bikin ba a kammala shi ba,” in ji ’yar uwar amaryar.

Amarya da angon dai duka sun ki yarda su yi magana da ‘yan jarida a kan lamarin, amma majiyoyin da ke da kusanci da su sun ce suna cikin kaduwa sosai.