✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Messi ya kulla yarjejeniya da PSG

Messi zai samu damar haduwa da tsohon abokin taka ledarsa, wato Neymar.

Shahararren dan kwallo kafar nan Lionel Messi, ya kulla yarjejeniya da Paris Saint-Germain, kwanaki kadan bayan rabuwarsa da Barcelona.

PSG mai buga gasar Ligue 1 ta Faransa, ta kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Messi inda za ta biya shi Fan miliyan 25 duk shekara bayan kudin haraji.

Yanzu haka dan wasan na kan hanyarsa ta zuwa birnin Paris tare da iyalansa.

Ana tsammanin zai sauka Kasar Faransa don rattaba hannu a kan kwantaragin wanda yake dauke da damar kara shekaru idan ya so hakan.

Lauyan Messi da mahaifinshi Jorge su ne suke tattaunawa da kungiyar ta PSG tun ranar Alhamis.

Zuwan Messi PSG zai ba shi damar sake haduwa da tsohon abokin wasan shi a Kungiyar Barcelona wato Neymar.

%d bloggers like this: