Shahararren dan kwallo kafar nan Lionel Messi, ya kulla yarjejeniya da Paris Saint-Germain, kwanaki kadan bayan rabuwarsa da Barcelona.
PSG mai buga gasar Ligue 1 ta Faransa, ta kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Messi inda za ta biya shi Fan miliyan 25 duk shekara bayan kudin haraji.
- Isa Abba Adamu: Ba rabo da gwani ba…
- Yadda aka ci zarafin jami’in diflomasiyyar Najeriyar A Indonesiya
Yanzu haka dan wasan na kan hanyarsa ta zuwa birnin Paris tare da iyalansa.
Ana tsammanin zai sauka Kasar Faransa don rattaba hannu a kan kwantaragin wanda yake dauke da damar kara shekaru idan ya so hakan.
Lauyan Messi da mahaifinshi Jorge su ne suke tattaunawa da kungiyar ta PSG tun ranar Alhamis.
Zuwan Messi PSG zai ba shi damar sake haduwa da tsohon abokin wasan shi a Kungiyar Barcelona wato Neymar.