✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MDD ta tabbatar da sace mata ’yan gudun hijira sama da 200 a Borno

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da rahoton Aminiya kan sace mata ’yan gudun hijira sama da 200 a Jihar Borno.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da rahoton sace mata ’yan gudun hijira kimanin 200 a Jihar Borno.

Majalisar ta soki sace ’yan gudun hijirar, wadanda yawancinsu mata ne, a Karamar Hukumar Ngala ta jihar.

Da yake tabbatar da cewa adadin ya haura 200, jami’i mai kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya “jajanta wa iyalai da dangin duk wadanda aka sace, musamman kananan yara, mata da tsofaffi.

“Sannan ina kira ga wadanda suka sace su da su gaggauta sakin su ba tare da wani lahani ba.

“A madadin Majalisar Dinkin Duniya, ina tunatar wadanda ke wannan mummunan aiki da su kiyaye, su bari.

“Bugu da kari, ina kira ga hukumomi da sauran abokan hulda da su dubi yanayin rayuwar ’yan gudun hijira da ke sansanoni a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Jami’in Majalissar Dinkin Duniyan ya ce “A halin da ake ciki fiye da mutane miliyan biyu daga jihohin Borno, Adamawa da Yobe ne suke gudun hijira a makwabtan jihohinsu.

“Kwana biyu da bikin tunawa da ranar mata ta duniya wannan lamari na cin zarafi ga matan ya faru, wannan na tunatar da mu cewa mata da ’yan mata suna cikin wadanda wannan matsala tafi shafa,” in ji jami’in.