Antonio Guteress, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci Rasha ta mika wuya ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), don gudanar da bincike a kanta kan yiwuwar aikata laifukan yaki a Ukraine.
Guteress ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai garin Bucha da ke makwabtaka da Kyiv, babban birnin Ukraine, inda ya ce akwai bukatar Rasha ta ba da hadin kai kotun ta gudanar da bincike yadda ya kamata.
- ’Yan bindiga sun bukaci man fetur da sigari a matsayin fansar basaraken da suka sace a Kaduna
- Masu kwacen waya sun raunata ma’aikaciyar Daily Trust a Kano
Ya ce idan ana maganar laifukan yaki, to babu ma abin da ya fi yakin kansa girma wajen laifi.
Garin na Bucha inda Guterres ya kai ziyara, nan ne a aka gano gawarwakin daruruwan fararen hula bayan sojojin Rasha sun janye daga garin.
Karon farko ke nan da babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya kai ziyara Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da hare-harenta a kan kasar.
Guterres ya bayyana yakin a matsayin rashin hankali da ya auku a karni na 21, inda ya bayyana yaki a matsayin abu mafi muni da tashin hankali.
A bangare guda kuma, masu shigar da kara na gwamnatin Ukraine sun fara bincikar wasu sojojin Rasha 10 da ake zargi da aikata laifukan yaki a Bucha.