Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kylian Mbappe zai yi jinyar sati uku, biyo bayan raunin da ji a ranar Talata.
Likitocin ƙungiyar sun tabbatar da cewar ɗan wasan ya samu rauni ne a wasan da Real Madrid ta doke Alaves da ci 3 da 2.
- Yajin Aiki: ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14
- Raphael Varane ya yi ritaya daga taka leda
Tuni Real Madrid ta fitar da sanarwa game da raunin da ɗan wasan ya ji.
Mbappe ba zai buga wasan da Real Madrid za ta yi da abokiyar hamayyarta, Atletico Madrid a ƙarshen mako mai zuwa.
Har wa yau, ɗan wasan ba zai buga wasanni bayan wasan hammayar na birnin Madrid da za a yi.