✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mbappe ya dawo atisaye gabanin karawar PSG da Bayern Munich

PSG da Bayern Munich za su barje gumi a Gasar Zakarun Turai a daren ranar Talata.

Dan wasan gaban PSG, Kylian Mbappe ya dawo atisaye bayan raunin da ya ji sati biyu da suka wuce.

Mbappe ya dawo atisayen ne gabanin karawar da PSG za ta yi da Bayern Munich a Gasar Zakarun Turai.

Mbappe ya ji raunin ne a ranar 1 ga watan Fabrairu, a karawar da PSG ta yi da Montpellier a gasar Ligue 1 ta Faransa, kuma aka kiyasta cewa zai yi sati uku yana jinya.

Sai dai a ranar Asabar kocin PSG, Christophe Galtier, ya ce ba ya tunanin Mbappe zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Bayern Munich a ranar Talata.

Sai dai Mbappe ya dawo daukar horo a ranar Lahadi, sannan a ranar Litinin an hange shi tare da taurarin PSG irinsu Messi da Neymar suna atisaye tare.

PSG dai na son ganin ta kafa tarihi wajen lashe Gasar Zakarun Turai a karon farko a tarihinta, bayan kashe maduden kudade wajen gina kungiyar.