✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

’Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne sun kashe mutum 17 a wani hari da suka kai a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie…

’Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne sun kashe mutum 17 a wani hari da suka kai a garin Mera da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi a ranar Jumu’a domin satar shanu.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen sun shigo garin Mera da misalin karfe 1 na dare suka saci shanun mutane da yawa.

A nan ne mutane suka yi kokarin kwato dabbobin, inda a harbin mai uwa da wabi suka kashe mutum 17, wandanda aka yi wa 15 daga cikinsu Sallah a lokaci guda a ranr Asabar.

Ganau din ya kara da cewa daga bisani aka ga gawar mutum biyu, inda su ma aka yi masu sutura aka kai su makwancinsu.

“Mun yi ba-ta-kashi da su ne, mun jikkata wasu daga cikin mutanensu, sai dai sun tafi da shanu da ’yan uwansu da suka samu rauni, haka mu ma wasunmu sun samu rauni, an kai su asibiti,” in ji shi.

Ya ce, garin Mera ba ya fama da matsalar tsaro, sai yanzun da wadannan ’yan bindigar suka shigo har suka tafi da shanunmu bayan sun kashe al’umma.

“An yi Sallar Jana’izar mutanen wadda Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida da Sarkin Argungu Sama’ila Muhammad Mera suka halarta.

“Bayan kammala yi wa marigayan sutura mataimakin gwamna ya kuma mika ta’aziyarsa ga iyalan mamatan tare da alkawalin hukunta wadanda suka yi wannan aika-aikar.”

Ya ce, “gwamnatin jiha za ta yi aiki sosai da jami’an tsaro don tabbatar da irin haka bai sake faruwa ba.

“Sarkin Argungu ya nemi al’umma su hada kansu a rika bayar da bayanin duk abin da ba a gamsu da shi ba a wajen jami’an tsaro don a tabbatar da an kare jama’a.