Mayakan kungiyar Al-Shabaab sun hallaka fararen hula akalla takwas a wani otel da ke Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya.
Hukumomin kasar sun ce mayakan sun yi garkwua da mutane da dama a otel din Al-Hayat, inda jami’an gwamnati da manyan mutane ke yawan gudanar da taruka.
- Kwamandan ’yan ta’adda zai auri fasinjar jirgin kasan Abuja-Kaduna
- ‘Ina rubutu da kafa domin ciyar da iyalina’
Wani kwamandan tsaro, Mohamed Abdikadir, ya ce, “Jami’an tsaro sun yi wa wurin kawanya kuma suna ci gaba da kawar da ’yan ta’addan, wadanda suka shige wani daki a otal din.
“An kubutar da yawancin mutanen da ke otel, amma fararen hula akalla takwas sun rasa rayukansu.”
A yammacin yararn Juma’a ne mayakan suka kutsa cikin otel din suna harbe-harbe da tayar da bama-bamai tare da yin garkuwa da mutanen da ke ciki.
A safiyar Asabar wani jami’in gwamantin kasar ya sanar cewa jami’an tsaro sun yi wa wurin kawanya da ’yan ta’addan suke kawanya domin murkushe shi.
Sai dai an yi ta jin karar harbi da fashewar bama-bamai har zuwa safiyar Asabar a otel din.
Harin dai shi ne mafi muni a Somaliya tun bayan zaben Shugaba Hassan Sheikh Mohamud, a watan Mayu, bayan rikicin siyasa a kasar.
Kungiyar Al-Shabaab dai ta dauki alhakin hare-haren da aka shafe sama da shekara 15 ana kai wa gwamnatin kasar.